Iran ta kai hari hedikwatar hukumar leƙen asirin Isra’ila
Published: 17th, June 2025 GMT
Kafofin yaɗa labarai na cikin gida a Iran sun yi iƙirarin cewa ƙasar ta kai hari kan hedikwatar hukumar leƙen asiri ta ƙasar Isra’ila (Mossad).
Kamfanin dillancin labaran Iran (TASNIM) ya ruwaito cewa rundumar juyin juya hali na Iran (IRGC) ce ta kai harin a hedikwatar Mossad da ke Herzliya.
Kamfanin ya wallafa wasu jerin hotuna da ya ce suna nuna yadda hedikwatar ta Mossad ke ci da wutan ne bayan harin makamai masu linzami ne da Iran ta kai mata.
Kafar yaɗa labarai ta Tehran Times ta ruwaito cewa hare-haren na IRGC sun ƙona wani ɓangare na cibiyar Aman, wanda wani ɓangare ne na ginin hukumar leƙen asirin asirin sojin Isra’ila ta Aman, da ke Glilot.
An garzaya da ’yan Isra’ila 154 asibiti bayan harin Iran Matatar man Isra’ila ta daina aiki bayan sabon harin Iran Sarki ya yi barazanar hana yin Musulunci a garinsa bayan dodanni sun kai wa Musulmi hariKawo yanzu dai ba a iya tantance sahihancin wannan iƙirarin na Iran ba daga kafofin yaɗa labarai da ke aiki a yankin; kuma hukumomin Isra’ila ba su ce uffan a kai ba.
A cewar hukumar kare haƙƙin ɗan’Adam a Iran (HRANA), fararen hula 224 ne suka mutu, yayin da 188 suka jikkata a hare-haren Isra’ila a ƙasar.
HRANA ta kuma bayyana cewa sojoji 109 ne suka mutu inda kuma 123 suka jikkata.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Manyan makarantu 2 ne kacal ke da rajista a Katsina — Gwamnati
Kwamitin da Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umari Radda, ya kafa domin binciken ayyukan makarantun gaba da sakanadare masu zaman kansu na jihar, ya tabbatar da cewa, 37 cikin 39 ba su da rajista da gwamnati.
Shugaban kwamitin, Farfesa Ahmed Muhammad Bakori, ne ya bayyana hakan a wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a ƙaramar hukumar Bakori da ke jihar.
Mamakon ruwan sama ya haddasa ambaliya a Maiduguri Sojoji sun daƙile hari, sun kashe mayaƙan Boko Haram 9 a BornoBakori, wanda shi ne Kwamishinan Harkokin Noma na jihar, ya ce binciken kwamitin ya gano cewa makarantu biyu masu zaman kansu ne kacal a faɗin jihar ke da cikakkiyar rajista da hukumomin da suka dace.
“Jihar Katsina na da makaruntun gaba da sakanadare na gwamnati huɗu da ke bayar da takardar shaidar difloma da koyarwa, sai kuma ƙarin 39 masu zaman kansu.
“Sai dai bincikenmu ya bankaɗo biyu ne kacal a cikin 39 suke da cikakkiyar rajista da hukumomi.”
Kwamishinan, ya kuma ce shida daga cikinsu na buƙatar gyare-gyare domin kammala rajistar, yayin da 22 ke aiki ba tare da rajistar ba.
“Ƙarƙashin sabon tsarin da muka ɗauka yanzu, ya zamo dole makarantun da ke bayar da takardar shaidar digiri su yi rajista da Hukumar Jami’o’i ta Ƙasa (NUC).
“Masu difloma kuma da Hukumar Kula da Ilimin Fasaha (NBTE), sai masu koyarwa da Hukumar Kula da Kwalejin Ilimi ta Ƙasa (NCCE).
Bakori, ya jaddada cewa, duk makarantar da ta saɓa wa wannan tsarin, a shirye gwamnatin take ta rufe ta.
Sai dai ya yi wa ɗaliban da ke makarantun albishir ɗin cewa gwamnatin za ta tabbatar ta sauya musu makaranta zuwa masu rajista daga waɗanda ba su da su, idan buƙatar rufe su ta taso.