Kungiyar malaman musulmi ta duniya ta yi kira da a tallafa wa Falasdinawa
Published: 6th, March 2025 GMT
Sakatare-janar na kungiyar malaman musulmi ta duniya ya yi kira ga shugabannin kasashen Larabawa da su hada kai da al’ummarsu wajen goyon bayan Falasdinawa.
Babban sakataren kungiyar malaman musulmi ta duniya Ali Muhammad Al-Salabi, ya yi kakkausar suka kan ci gaba da goyon bayan da Amurka ke yi wa haramtacciyar kasar Isra’ila, yana mai bayyana hakan a matsayin taka rawa a cikin laifukan da take aikatawa kan al’ummar Palastinu.
Ya yi nuni da cewa, wannan tallafin na nuni da nuna son kai na siyasa da ke neman boye laifukan kisan kare dangi take aikatawa kan fararen hular zirin Gaza da ba su da kariya.
A cikin jawabinsa, Al-Salabi ya yi kira ga gwamnatocin kasashen Larabawa da na Musulunci da su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na tarihi, tare da ba da goyon baya ga al’ummar Palastinu.
Babban sakataren kungiyar kasashen musulmi ta duniya ya jaddada cewa, alhakin ceto al’ummar Palastinu, bisa la’akari da goyon bayan da manyan kasashen duniya suke bayarwa ga gwamnatin sahyoniyawan ya rataya a wuyan gwamnatocin musulmi, da kasashen Larabawa da kuma ‘yantattun al’ummomi naduniya.
Haka nan kuma ya yi kira ga muhimman cibiyoyin Musulunci karkashin jagorancin Al-Azhar da su yi amfani da dukkan hanyoyin da ake da su na matsin lamba wajen ceto Falasdinawa.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: musulmi ta duniya
এছাড়াও পড়ুন:
Har Yanzun Ana Zaman Dar-Dar A Burkina Faso Bayan Kokarin Juyin Mulkin Da Bai SamiNasara Ba
Ana ci ga ba da zaman dar-dar a kasar Burkina faso, bayan da shugaban kasa mai ci Ibrahim traure ya sake tsallaka rijiya da baya, a wani kokarin juyin mulki wanda bai sami nasara ba a makon da ya gabata.
Shafin yanar gizo na labarai ‘Africa News’ya nakalto radiyo Faransa RFI yana fadar cewa an bankado juyin mulkin ne bayan da dukkan bakin da aka gayyata a ranar 22 ga watan Afrilu zuwa wani taro sun kasa halattan taron. Wanda ya nuna shakku kan abinda aka kulla a cikin taron.
Labarin ya kara da cewa a cikin yan kwanaki masu zuwa mutanen kasar zasu fito zanga-zanga don nuna goyon bayansu ga shugaban Traore.
Har’ila yau ana gudanar da bincike a cikin barikokin sojojin kasar a birnin Wagadugu a kokarin gano wadanda suke adawa da gwamnatin Traore, sannan suke aiki wa kasashen yamma musamman kasar Faransa wajen ganin bayan shugaba Ibrahim Traore.
Kafin haka dai an nakalto ministan tsaron kasar ta Burkina faso Muhammada Sana ya na wani bayani a tashar talabijin na kasar, kan cewa kafin su gano shirin juyin mulki sun satar maganar wayar tarho tsakanin wani babban sojan kasar da shugaban wata kungiyar ta’addaci wanda aka shirya za su kashe shugaba Traore.