Nijeriya za ta fara fitar ta tataccen mai zuwa Asia — Matatar Dangote
Published: 18th, June 2025 GMT
A karon farko Nijeriya za ta fara fitar da tataccen man fetur zuwa nahiyyar Asia kamar yadda wata majiya daga Matatar Dangote ta sanar.
Majiyar ta ce wani jirgin ruwan dako mai ɗauke da tan 90,000 na man fetur zai yi jigilar daga Matatar Dangote da ke Nijeriya zuwa nahiyar Asia.
HOTUNA: Yadda Tinubu ya ziyarci waɗanda suka jikkata a harin Benuwe Hare-haren Benuwe: Tinubu ya ziyarci waɗanda suka jikkata a asibitiKamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya ambato majiyar wadda ta buƙaci a sakaya sunanta tana cewa “yanzu jirgin ruwan Mercuria zai tafi Asia a ranar 22 ga Yuni.
“Muna sayar da kayanmu ne ga waɗanda suka yarda su ba mu farashi mafi yawa. Mai saye na da haƙƙin kai wa duk inda yake so,” in ji kakakin matatar mai ta Dangote.
Darektan a kamfanin Horizon Engage, Clementine Wallop, ya alaƙanta fitar da man da matatar za ta yi a matsayin wani gagarumin tasiri na zama abar dogaro wajen samar da mai a faɗin duniya.
Tun bayan da matatar mai karfin tace ganga 650,000 na ɗanyen mai a kowacce rana ta fara fitar da fetur a bara, jiragen ruwan da ke ɗaukar man zuwa Yammacin Afirka ne.
Matatar man ta dala biliyan 20 da mai kuɗin Afirka Aliko Dangote ya samar a birnin Legas, ta fara aiki a watan Janairun shekarar da ta gabata.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Matatar Dangote Nahiyar Asiya
এছাড়াও পড়ুন:
Ɗaliban da aka sace a Binuwai sun kuɓuta
Jami’an tsaro sun tabbatar da kuɓutar wasu ɗalibai shida na Makarantar Horon Ilimin Shari’a ta Najeriya da aka sace.
Rundunar ’yan sandan Jihar Binuwai ce ta bayyana hakan a ranar Juma’a.
’Yan Najeriya miliyan 34 na cikin barazanar yunwa Mun ci ribar Naira biliyan 414 a cikin wata 6 a Najeriya – Kamfanin MTNKakakin ’yan sandan, Udeme Edet, ya ce ɗaliban sun taso ne daga Jihar Anambra, yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa makarantar horon ilimin shari’a da ke Yola, a Jihar Adamawa.
’Yan bindiga ne suka tare su a iyakar Binuwai da Taraba.
“An ceto ɗalibai shida da aka sace a ranar 26 ga watan Yuli, 2025, yayin da suke kan hanyarsu daga Anambra zuwa Adamawa.
“An sako su lafiya ƙalau kuma sun koma wajen iyalansu a safiyar yau, 1 ga watan Agusta, 2025,” in ji sanarwar.
Maharan sun nemi Naira miliyan 120 a matsayin kuɗin fansa, kuma sun yi barazanar kashe ɗaliban idan ba a biya buƙatarsu ba.
Matsalar na ci gaba da ta’azzara a Jihar Binuwai.
A bara ma, an sace ɗalibai 20 yayin da suke kan hanyar zuwa Jami’ar Jos a Jihar Filato.
Maharan sun sako su bayan shafe makwanni a hannunsu.