Ambaliyar Mokwa – Har yanzu muna neman mutum 700 – Gwamnatin Neja
Published: 18th, June 2025 GMT
Gwamnatin jihar Neja ta ce har yanzu akwai sama da mutum 700 da suka bace ba gan su ba tun bayan mummunar ambaliyar ruwan da aka yi a karamar hukumar Mokwa da ke jihar.
Gwamnan jihar, Mohammed Umar Bago ne ya bayyana hakan lokacin da ya karbi babban dogarin tsohon Shugaban Kasa marigayi Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha yayin ziyarar jaje kan ambaliyar a Minna ranar Talata.
Gwamnan, wanda mataimakinsa, Yakubu Garba ya wakilta ya kuma ce akalla mutum 207 ne aka tabbatar da mutuwarsu sannan gidaje sama da 3,000 ne suka rushe.
DAGA LARABA: Ko Kare Kai Daga Harin ‘Yan Ta’adda Zai Kawo Karshen Matsalar Tsaro? Jirgin alhazai ya yi saukar gaggawa kan barazanar harin bom“Sama da mutum 700 ne suka bace kuma ba a san inda suke ba. Wannan ambaliyar ta jawo mana babbar asara,” in ji shi.
Ya kuma yaba wa hukumomi da kamfanoni da ma daidaikun jama’a da suka ba da tallafi, inda ya ce iftila’in annoba ce ta kasa baki daya.
Gwamnan ya kuma ce yanzu haka gwamnatin na dakon sakamakon binciken hukumomi kan musabbabin ambaliyar da hanyoyin kauce mata a nan gaba.
Tun da farko, Al-Mustapha ya ce ya je jihar ne domin jajanta mata kan mummunar ambaliyar ta Mokwa
“Za mu gana da masu rike da sarautun gargajiya da musamman Ciyaman din karamar hukumar ta Mokwa domin mu yi musu addu’ar kare faruwar hakan a nan gaba,” in ji shi.
Ya kuma ce tawagar jajen tasu ta kunshi muhimman mutane daga sassa daban-daban na kasar nan domin jajantawa da bayar da tallafi ga gwamnati da yankunan da ta shafa.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Sabon Tsarin Kula Da Lafiyar Mata Masu Juna Biyu Da Kananan Yara
Gwamnatin Jigawa ta amince da sabon tsarin ka’idojin aiki domin aiwatar da shirin kula da lafiyar mata masu juna biyu, da jarirai da ƙananan yara kyauta a cibiyoyin lafiya na jihar.
Kwamishinan Yaɗa Labarai, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ya bayyana haka bayan zaman majalisar zartarwa da aka gudanar a gidan gwamnati Dutse.
Ya ce ka’idojin za su taimaka wajen inganta nagartar hidima, fayyace karewar ma’aikata, da kuma tabbatar da gaskiya, da bin doka da tsari a asibitoci.
Kwamishinan ya ƙara da cewa matakin ya dace da manufar gwamnatin jihar na rage mace-macen mata da yara da kuma tabbatar da samun ingantacciyar kulawa ga kowa.
Ya ce za a fara aiwatar da tsarin nan take, tare da horas da shugabannin asibitoci da cibiyoyin lafiya na ƙananan hukumomi domin cimma nasarar shirin .
Usman Muhammad Zaria
—
Kana so in ƙara ɗan salo na labarin jarida (irin rubutun kafafen yaɗa labarai) ko a barshi haka cikin sauƙin bayani?