Sauran sun hada da: Danjuma Azi, Fwangje Bala Ndat, Salome Tanimu Wanglet, Namba Rimuyat, Nimchak Rims, Ishaku Maren da Paul Datugun.

 

Kakakin hukumar ta EFCC, Dele Oyewale, wanda ya tabbatar da kamun, ya ce bincike ya nuna cewa tsaffin ‘yan majalisar sun shafe watanni shida ne kawai a kan karagar mulki, sannan gwamnatin jihar ta siya musu motocin alfarma.

 

 

Bincike ya kuma nuna cewa, motocin da aka ce kudinsu ya kai Naira biliyan 2.5. Bayan sun sauka akan mukaminsu, sun tafi da motocin kuma duk kokarin da aka yi na su dawo da su, lamarin ya ci tura.

 

Sai da gwamnatin jihar ta sake sayo wa ‘yan majalisar na yanzu motocin da kudinsu ya kai kimanin naira biliyan biyu.

 

Oyewale ya tabbatar da cewa nan ba da jimawa ba za a gurfanar da tsohon shugaban majalisar da sauran mambobin a kotu.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Saudiyya ta saki ’yan Najeriya 3 da ta kama kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi

Hukumomin a Ƙasar Saudiyya, sun saki wasu ’yan Najeriya uku da aka kama a Jeddah kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi.

Waɗanda aka saki sun haɗa da Hajiya Maryam Hussain Abdullahi, Hajiya Abdullahi Bahijja Aminu, da Malam Abdulhamid Saddieq.

Tinubu bai shirya gudanar da sahihin zaɓe ba a 2027 – Buba Galadima Gwamnati ta fara duba yara marasa galihu kyauta a asibitin Aminu Kano

Sun shafe makonni huɗu a tsare kafin aka tabbatar da cewa ba su da laifi.

A wajen taron manema labarai a Abuja, mai magana da yawun Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA), Femi Babafemi, ya ce sakin ya biyo bayan tttaunawa da Shugaban NDLEA, Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya), tare da Hukumar Hana Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Saudiyya.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne, ya bayar da cikakken goyon baya wajen ganin an saki waɗanda aka kama.

Bincike ya gano cewa wasu masu safarar miyagun ƙwayoyi ne a Filin Jirgin Sama na Mallam Aminu Kano, suka ƙwayoyin a jakunkuna waɗanda aka kama.

Mutanen uku da aka kama, sun tashi a jirgin Ethiopian Airlines a ranar 6 ga watan Agusta don yin Umara, amma aka kama su a Saudiyya.

Binciken NDLEA ya kai ga kama wani shugaban masu safarar miyagun ƙwayoyin, mai shekaru 55, Mohammed Ali Abubakar (wanda aka fi sani da Bello Karama).

Hakazalika, hukumar ta kama wasu mutum uku ciki har da ma’aikatan jirgi.

Mutanen da aka kama su ne suka shirya safarar ƙwayoyin a jakunkunan mutane da aka kama a Saudiyya.

NDLEA ta gabatar da shaidun da suka tabbatar da cewa mutanen da aka kama a Saudiyya ba su da laifi.

Sakamakon haka, hukumomin Saudiyya suka sako ɗaya daga cikinsu a ranar 14 ga watan Satumba, sannan suka sako sauran biyun a ranar 15 ga watan Satumba.

Babafemi, ya ce Marwa ya gode wa hukumomin Saudiyya saboda mutunta yarjejeniyar haɗin kai tsakaninsu da Najeriya.

Ya kuma gode wa Shugaba Tinubu da sauran manyan jami’an gwamnati, ciki har da Ministan Shari’a, Ministan Harkokin Ƙasashen Waje, Ministan Sufurin Jiragen Sama, da Mai Bai Wa Shugaba Shawara Kan Harkar Tsaro, saboda gudummuwarsu.

Ya ƙara da cewa wannan lamari ya nuna cewa Najeriya tana tsayawa wajen kare ‘yan ƙasarta a ƙasashen waje kuma ba za ta yadda wani ɗan Najeriya ya sha wahala saboda laifin da bai aikata ba.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Ta Kammala Ziyarar Yini 3 A Ma’aikatar Kananan Hukumomin Jihar
  • Tinubu Ya Janye Dokar Ta-baci A Jihar Rivers
  • ‘Yansanda Sun Kama Mutane 6 Kan Zargin Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ƙa’ida Ba A Neja
  • Saudiyya ta saki ’yan Najeriya 3 da ta kama kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi
  • Ana zargin mace da kashe ’yar uwarta a kan N800 din barkono
  • Kakakin Majalisar Jigawa Ya Tsallake Rijiya Da Baya, Tawagar Jami’an Tsaronsa Sun Ji Rauni A Wani Hatsari A Jihar 
  • Majalisar Dattawa Ce Kawai Za Ta Iya Dawo Da Sanata Natasha – Magatakardar Majalisa
  • NDLEA ta kama ɗan Indiya da ƙwaya ta Naira biliyan 3 a Legas
  • Ɗan Majalisar Tarayya Ya Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-haren Ta’addanci A Sakkwato 
  • An kama tsohon minista kan zargin kisan kai domin tsafi a Nijar