Shugabannin Duniya Za Su Gudanar Da Taron Sanya Hannun Jarin Bunƙasa Ƙudurorin Muradun Ƙarni A Sifaniya
Published: 16th, June 2025 GMT
Shirin dai zai kunshi abubuwa masu mahimmanci guda uku;
Na farko, Taron Sevilla zai taimaka wajen zaburar da shigowar tallafi zuwa ga kasashen da suka fi bukatarsa.
Na biyu, dole ne kasashe su kasance a kan kujerar tattara albarkatun cikin gida ta hanyar karfafa samar da kudaden shiga da magance rashin biyan haraji, hadin gwiwar kasa da kasa.
A bangare daya kuma, akwai bukatar bankunan ci gaban kasa, da na shiyya-shiyya da kuma bankunan raya kasa-da-kasa, su hada hannu domin saka manyan jari.
Domin tallafa wa wannan shirin bayar da lamuni na wadannan bankunan, akwai bukatar a ninkawa sau uku ta yadda kasashe masu tasowa za su iya samun babban jari ba tare da an dora masu ruwa mai yawa ba.
Hakan zai bayar da damar ajiyar dukiya a asusun waje ba tare da wasu sharuda masu tsauri ba ko damar gudanar da al’amura a kasashe masu tasowa.
A ko’ina, masu bayar da tallafi dole ne su cika alkawuransu na kawo ci gaba, kuma dole ne a gyara tsarin bayar da bashi, domin akwai rashin adalci da yaudara a tsarin.
Daga karshe, dole ne taron Sevilla ya tsawatar tare da karfafa kasashe masu tasowa a tsarin kudi na duniya domin biya musu bukatunsu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jihar Kano Ta Kaddamar da Manufar Sauyin Yanayi
Gwamnatin jihar Kano tare da hadin gwiwar wata kungiya mai suna Partnership for Agile Governance and Climate Change (PACE) ta kaddamar da manufofinta na sauyin yanayi a hukumance. Wannan manufa mai mahimmanci ta samar da taswirar dabaru don ragewa, daidaitawa, da tsarin tafiyar da yanayi mai hadewa a duk sassan ci gaba a jihar.
Da yake jawabi a wajen taron kaddamar da taron wanda aka gudanar a dakin taro na Armani Event Centre dake Kano, Gwamna Abba Yusuf wanda sakataren gwamnatin jihar Ibrahim Farouk ya wakilta, ya bayyana taron a matsayin wani babban ci gaba a kokarin gwamnatinsa na mayar da jihar Kano a matsayin mai ci gaba a harkokin tafiyar da yanayi da muhalli.
Gwamna Yusuf ya jadadda cewa, manufar tana cike da shirin aiwatar da sauyin yanayi, wanda ke fassara kudirin siyasar gwamnati zuwa tsarin aiwatarwa a aikace.
Ya kuma yi tsokaci kan shirye-shiryen da gwamnati ke yi na samar da makamashi ta hasken rana da ababen more rayuwa.
Gwamnan ya nanata shirin gwamnatin sa na dasa itatuwa miliyan 5 a shekarar 2025 domin rage zaizaiyar kasa, da inganta iskan shaka, da inganta kyawawan birane.
ABDULLAHI JALALUDDEEN KANO