Sarki ya yi barazanar hana yin Musulunci a garinsa bayan dodanni sun kai wa Musulmi hari
Published: 17th, June 2025 GMT
Sarkin yankin Oke Agbe a Jihar Ondo ya ci Musulmi tara, tare da barazanar koran su da kuma haramta yin addinin Musulunci a garinsa bayan da wasu dodanni suka kai hari a wani masallaci da gidan limami.
Aminiya ta samu rahoto cewa, wasu dodanni sun kai hari a masallaci da gidan wani limami, suka lakaɗa wa matansa da ’ya’yansa duka a yankin Oke Agbe, da ke shiyyar Akoko a Ƙaramar Hukumar Akoko ta Arewa a Jihar Ondo Jihar Ondo.
Ƙungiyar Kare Haƙƙin Musulmi (MURIC), ta bayyana cewa, “Basaraken yankin ya yi Musulmin tara da aka ci zalinsu tara, saboda sun yi ihu tare da zagin dodannin, maimakon su riƙa yin kuka suna roƙon dodannin.
“Basaraken ya umarci matan limamin su biya tarar awaki tara da tumaki bakwai da kuma ƙwarya biyu na hoto, cikin kwana uku, kafin ranar Litinin da ta gabata, ko kuma a haramta musu zama a garin.”
Ɗan shekara 10 ya harbe mahaifinsa ɗan sanda a Anambra Yadda Cin ganyayyaki ke gagarar ’yan NajeriyaShugaban Ƙungiyar, Farfesa Ishaq Akintola, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, dodannin sun kai wannan harin ne a ranar Alhamis 12 ga watan Yuni, nan da muke ciki.
Farfesa Ishaq Akintola, ya bayyana harin a matsayin wata shaida da ke nuna yadda ake tsananin cin zarafin Musulmi a yankin Yarabawa, don haka ya kira da a ɗauki matakin shari’a a kan duk masu hannu a wannan aika-aika.
Ya ci gaba da cewa abin da ya faru ya ƙara girman fargabar da ƙungiyar take da shi gane da makomar al’ummar Musulmi a yankin Kudu maso yammacin Najeriya, “saboda abin sai ƙara muni yake ta yi.”
Don haka muna Allah-wadai da wannan hari na jahiliyya, da kuma zaluncin wannan sarki, wanda ya ci karo da kundin tsarin mulkin ƙasa, a ƙarƙashin tsarin dimokuraɗiyya a ƙarni na 21.
“Muna kira da a yi wa waɗannan Musulmi adalci, kuma muna kira ga Gwamnatin Jihar Ondo ya taka wa Sarkin Oke Agbe Akoko bukri, tare da tabbatar da cewa wani abin ƙi bai samu limamin ko ’ya’yansa ko matansa ba. Sa’annan dole a janye maganar haramta musu zama a garin,” in ji kungiyar Musulmin.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Yan Nijeriya Na Ɗanɗana Kuɗarsu Kan Jinkirta Cire Tallafin Mai – Sarki Sanusi
“A lokacin, mun yi lissafin adadi a Babban Bankin. Na tashi na kafa sharuda bisa ga ka’idodi, inda na ce a cire tallafin yau. Farashin kaya zai tashi daga kashi 11 zuwa kashi 13, zan rage shi a cikin shekara guda. Ba za mu samu hauhawar farashin kaya na kusan kashi 30 ba,” in ji shi.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA