Xi Ya Gabatar Da Muhimmin Jawabi A Taron Koli Na Sin Da Kasashen Tsakiyar Asiya Karo Na Biyu
Published: 17th, June 2025 GMT
A yau Talata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da muhimmin jawabi a taron koli na kasar Sin da kasashen yankin tsakiyar Asiya karo na biyu.
A cikin jawabinsa, Xi ya ce, yayin da kasar Sin da kasashe biyar na yankin tsakiyar Asiya ke tafiya kan hanyar samun ci gaba a cikin dogon lokaci, sun kafa “Ruhin Sin da kasashen tsakiyar Asiya” na “Mutunta juna, da amincewa da juna, da moriyar juna, da taimakon juna, da inganta zamanantarwa tare ta hanyar samun ci gaba mai inganci”.
Yayin da ya ambaci yanayin rashin kwanciyar hankali da duniya ke fama da shi, ya ce ta hanyar tabbatar da adalci ne za a iya cimma burin kare zaman lafiya, da samun ci gaban kasashe daban daban na bai daya a duniya. Kana ra’ayi na kashin kai, da kariyar ciniki, da na kashin dankali, ba za su amfani kowa ba.
Daga baya, shugaban ya yi kira da a karfafa hadin kan Sin da kasashe 5 dake tsakiyar Asiya, don kiyaye al’adarsu ta yarda da juna, da nuna wa junansu goyon baya, da zurfafa hadin gwiwarsu kan harkoki daban daban, da kare zaman lafiya, da karfafa musaya a fannin al’adu, gami da tabbatar da wani tsarin kasa da kasa mai adalci da daidaituwa a duniya. (Bello Wang, Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: tsakiyar Asiya
এছাড়াও পড়ুন:
Za A Bude Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Koli Na 20 Na JKS A Watan Oktoban bana
Yau Laraba 30 ga wata, an kira taro a ofishin siyasa na kwamitin koli na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin (JKS), inda aka yanke shawarar gudanar da cikakken zama na 4 na kwamitin koli na 20 na JKS a watan Oktoba na shekarar da muke ciki, domin nazari kan shawarar tsara shirin shekaru biyar-biyar na bunkasa tattalin arziki da zamantakewar kasar Sin na 15.
Taron ya nuna cewa, lokacin gudanar da “Shirin shekaru biyar-biyar din na 15”, lokaci ne mai muhimmanci a fannin tabbatar da ingantaccen tushe, da kokarin raya zamanantar da kasar Sin bisa tsarin gurguzu. A yanzu haka yanayin ci gaban kasar Sin yana fuskantar manyan sauye-sauye masu sarkakiya, akwai kuma damarmaki bisa manyan tsare-tsare da ma kalubale tare.
A waje guda kuma, tattalin arzikin kasar yana da tushe mai karko, da tarin fifiko, da karfin juriya, da kuma makoma mai kyau a nan gaba. Har ila yau, fifikon da kasar Sin ke da shi a fannonin tsarin gurguzu mai halin musamman irin na kasar, da kasuwa mai girma sosai, da cikakken tsarin masana’antu, da kuma albarkatun kwararru, ya fi bayyana sosai.
Taron ya kuma nuna cewa, kamata ya yi a kara azamar cimma nasara, da gudanar da ayyuka yadda ya kamata, don samun rinjaye bisa manyan tsare-tsare a yayin da Sin ke shiga takara a duniya, da ma samun babban ci gaba a ayyukan da suka shafi zamanantarwa irin ta kasar Sin. (Mai fassara: Bilkisu Xin)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp