Kotun Amurka ta daure ’yan Najeriya 5 shekaru 159 kan aikata damfara
Published: 19th, June 2025 GMT
Wata kotu a kasar Amurka ta yanke wa wasu ’yan Najeriya su biyar hukuncin daurin shekaru 159 bisa samun su da da laifin damfarar Amurkawa sama da 100.
Kotun dai ta sami mutanen ne da laifin damfarar kamfanoni da hukumomin gwamnatin kasar kudin da yawansu ya kai Dala miliyan 17, kwatwankwacin Naira biliyan 27 da miliyan 200.
Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sashen shari’a na kasar ya wallafa a shafinsa na intanet ranar Laraba, mai dauke da sa hannun mai rikon mukamin Babban Lauyan gwamnati na gundumar gabashin Texas, Ray Combs.
’Yan bindiga sun kashe manoma 24 a Katsina Yadda manoma suka yi addu’ar roƙon ruwa a ZamfaraSanarwar ta ce mutanen da aka yanke wa hukuncin sun hada da Damilola Kumapayi, Sandra Iribhogbe, Edgal Iribhogbe, Chidindu Okeke and Chiagoziem Okeke, kuma mambobi ne a wani gungun ’yan damfara na kasa da kasa.
Lauyan ya ce ’yan damfarar sun fara harkallar ne tun a shekara ta 2017, inda suke hakon tsofaffi da kuma masu rangwamen gata ta hanyar kirkiro dabaru daban-daban na karbar kudi daga wajensu, wasu lokutan ma ilahirin abin da suka tara a rayuwarsu.
“Da zarar sun karbi kudade daga mutane ta hanyar damfarar, sai su tuttura su ta hanyar asusun ajiya a bankuna da dama da kuma abokan harkallarsu da ’yan kasuwa da ke kasashe a nahiyoyin Afirka da Asiya,” in ji lauyan na gwamnatin Amurka.
Sanarwar ta ce bayan kama su, an gurfaran da su a gaban kotu kan laifukan da suka hada da hadin baki, zambar kudade da kuma damfara, wadanda dukkansu suka amsa aikatawa.
A cewar sanarwar, hakan ce ta sa alkalin kotun, Mai Shari’a Amos Mazzant, ya yanke musu hukuncin daurin shekaru daban-daban a kurkuku.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yan Najeriya Damfara
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Yadda Talauci Ke Hana Shayar Da Yara Nonon Uwa Zalla A Najeriya
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Ga alama kwalliya ba ta biyan kuɗin sabulu a fafutukar da ake yi ta ganin iyaye mata sun shayar da jariransu nono zalla a wata shida na farko.
Rahotanni sun ce duk da daɗewar da aka yi ana wayar da kai har yanzu matan da suke shayar da yara nono uwa zalla ba su haura kashi 29 cikin ɗari ba.
NAJERIYA A YAU: Me dokar kasa ta ce kan karin wa’adin aiki da Shugaban Kasa ke yi? DAGA LARABA: Dalilan al’ummomi na rungumar gwaji kafin aureShirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan dalilan da suke hana mata shayar da ’ya’yansu nono zalla na watanni shida.
Domin sauke shirin, latsa nan