Iran ta rataye mutumin da ta kama yana yi wa Isra’ila leƙen asiri
Published: 16th, June 2025 GMT
Iran ta ce ta aiwatar da hukuncin kisa ta hanyar rataya ga mutumin da aka kama yana yi wa Isra’ila leƙen asiri.
Mahukunta a bangaren shari’ar sun ce an kama Esmail Fekri a shekarar 2023 yana ƙoƙarin miƙa wa Isra’ila bayanan sirri ne don samun kuɗi.
KADSEMA da IOM sun fara tantance ɓarnar da ambaliya ta yi a Kaduna Sabon harin Iran ya hallaka mana mutum 8 – Isra’ilaWannan ne karo na uku a baya-baya nan da Iran ke aiwatar da hukuncin kisa saboda zargin leƙen asiri ga Isra’ila.
A ranar Lahadi, Isra’ila ta ce ta kama wasu ’yan ƙasa biyu da ake zargin suna aiki da hukumar leƙen asirin Iran.
Babban alƙalin Iran, Gholamhossein Mohseni Ejei, ya bayyana a ranar Litinin cewa, la’akari da yanayin “yaƙi” da suke ciki, dole ne a gudanar da shari’o’i ga waɗanda ake zargin suna aiki da Isra’ila cikin hanzari.
Bayan shafe gomman shekaru ana sa-in-sa tare da nuna wa juna yatsa, a ranar Juma’ar da ta gabata Israila ta kaddamar da wani farmaki na ba-zata wanda ta ce tana kai hari kan makaman nukiliyarta.
Kawo yanzu dai rayukan mutane 224 sun salwanta a kasar ciki har da manyan dakarun sojoji, kwararrun manazarta kimiyyar makaman nukiliya da kuma fararen hula.
Sai dai tuni ita ma Iran din ta mayar da martani tana mai luguden wuta ba dare ba rana a kan Isra’ila da zuwa alkaluman da ofishin firaiministan kasar ya fitar sun ce rayukan mutane akalla 24 sun salwanta.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Iran, ta yi wa Isra’ila ruwan makamai masu linzami
Iran ta kaddamar da wasu jerin hare-haren makamai masu linzami kan Isra’ila a matsayin maida martani kan haren haren da Isra’ila ta kai wa kasar a cikin daren ranar Juma’a.
Bayanai sun ce hare-haren na Iran sun lalata gine-gine da dama da jikkata mutane yayin da wasu rahotannin ke cewa an samu hasarar rayuka na akalla mutum biyu.
A cewar rahotannin kafofin yada labaran Isra’ila daban-daban, makamai masu linzami na iran sun fada a yankunan Tel Aviv, Haifa, Beersheba da wasu wurare.
An bayar da rahoton barna mafi muni a birnin Tel Aviv, inda akalla makami mai linzami guda ya afkawa wani bene mai hawa 50, lamarin da ya janyo fashewar wani abu mai karfi wanda ya sa hayaki ya tashi a sararin samaniyar birnin.
A cewar darektan cibiyar nazarin dabarun da huldar kasa da kasa, Amir Al-Mousawi, daya daga cikin makami mai linzamin na Iran ya afkawa wata cibiyar binciken nukiliya da ke birnin Tel Aviv.
Wasu rahotanni sun ce an kuma yi nasarar kaiwa ma’aikatar harkokin sojan Isra’ila hari.
Gwamnatin kasar ta sanya takunkumi, inda ta umarci mazauna yankin da kada su buga hotuna ko bidiyo na wuraren da makami mai linzami na Iran ya kai hari, kamar yadda kafar yada labaran Isra’ila ta bayyana.
Birgediya Janar Ahmad Vahidi, da yake magana da gidan talabijin na iran, ya ce martanin na iran mai lakabin Operation True Promise III “zai ci gaba muddin akwai bukatar hakan,” yayin da ya sha alwashin daukar fansar jinin shahidai.
Tun da farko, Vahidi ya ce an kai hari a kalla wurare 150 a harin ramuwar gayya kan gwamnatin Isra’ila, ciki har da wasu sansanonin soji masu matukar muhimmanci.