DAGA LARABA: Ko Kare Kai Daga Harin ‘Yan Ta’adda Zai Kawo Karshen Matsalar Tsaro?
Published: 18th, June 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Hare haren ‘yan ta’adda na kara ta’azzara a yankuna daban daban na fadin kasar nan wanda hakan ke nuni da Karin rashin tsaro da ya dade yana ciwa alumma da ma gwamnati tuwo a kwarya.
Ko a kwana kwanan nan an ga yadda jihar filato tayi ta fama da irin wadannan hare hare da kuma hare haren ramuwar gayya.
Wani kididdiga kungiyar dake tattara bayanan hare haren ta’addanci ta fitar ya nuna cewa Najeriya ta taso daga mataki na 8 zuwa na 6 a batun ta’addanci a duniya.
Kazalika a kwanakin nan wani hari da aka kai a wasu yankunan jihar Binuwe yayi sanadiyyar halakar mutane da dama, wadda hakan ya jawo cece ku ce da ya kai har wasu na kiran mutane su tashi don kare kan su.
Irin wannan kira dai an dade ana yi, sai dai gwamnati na ganin ba daidai ne mutane su kare kan su daga hare haren ‘yan ta’adda ba.
NAJERIYA A YAU: Yadda Cin Ganyayyaki Ke Yi Wa ‘Yan Najeriya Wahala DAGA LARABA: Dalilan Rashin Jituwa Tsakanin Marasa Lafiya Da Jami’an Kiwon LafiyaShirin Daga Laraba na wannan mako zai yi nazari ne kan shin ko kare kai daga hare haren ‘yan ta’adda zai kawo karshen matsalar tsaro da ake fuskanta a Najeriya?
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Dakile Hare hare hare hare kare kai matsalar tsaro
এছাড়াও পড়ুন:
Al’ummar Kauru Sun Koka Game Da Karuwar Hare-hare Da Ke Barazana Ga Gonaki Da Rayuka
Daga Yusuf Zubairu Kauru
Al’ummar Karamar Hukumar Kauru ta Jihar Kaduna sun shiga halin kaka-ni-ka-yi duba da yadda rayukansu ke kasancewa cikin hadari yayin da suke gonakinsu.
A wata tattaunawa ta wayar tarho, wani jagoran matasa, Junaidu Ishaq, ya bayyana cewa kusan shekaru biyar ke nan da hare-haren ’yan bindiga ke ta faruwa akai-akai, wanda ya bar al’umma cikin fargaba da ƙuncin rayuwa.
Ya ce manoma suna shiga gonakinsu ne cike da fargaba domin komi na iya faruwa yayin da suke aiki a gonakin.
Mazauna yankin sun bayyana cewa Kauru, wadda aka fi sani da yawan gonaki da ke taka muhimmiyar rawa wajen samar da abinci a jihar Kaduna, yanzu manoma ba sa iya shiga gonakinsu cikin kwanciyar hankali saboda yadda ‘yan bindiga ke yawan kai musu hare-hare.
A koda yaushe iyayen yara suna fargaba kada ‘ya’yansu su yi nesa da su, yayin da iyalai da dama da ke fama da ƙangin talauci ke kara shiga cikin matsanancin hali.
Sun yi kira gwamnati da hukumomin tsaro su yi gaggawar kai ɗauki wanda zai bai wa manoman karkara kwarin gwiwa, waɗanda su ne ginshiƙin samar da abinci a yankin.
Mazaunan sun yi gargadin cewa idan ba a ɗauki mataki cikin gaggawa ba, hare-haren na iya haifar da ƙaruwar matsalar rashin abinci da yawaitar ƙaura daga yankin.
“Idan zuwa gona zai sa mutumya rasa ransa, to lalle akwai babban matsala,” in ji wani manomi a yankin.
Sun yi fatan cewa za a dawo da zaman lafiya a yankin, yadda ƙasar da Allah Ya albarkace su da ita za ta ci gaba da ciyar da al’ummar Kauru ba wurin binne su ba.