Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Ɗaliba ’yar shekara 15 daga Yobe ta lashe Gasar Muhawara ta Duniya

Wata ɗaliba ’yar shekara 15 daga Jihar Yobe, Rukayya Muhammad Fema, ta zama Gwarzuwar Shekarar 2025 a Gasar Muhawara ta Duniya ta Teen Eagle.

Rukayya ta yi zarra ne a wannan babbar gasa da ta gudana a birnin Landan na ƙasar Birtaniya, inda zaƙaƙuran ɗalibai daga ƙasashe 69 a faɗin duniya suka fafata a tsakaninsu.

Jami’in Sadarwar Zamani na Gwamnatin Jihar Yobe, Yusuf Ali, ya bayyana cewa Rukayya ta samu kafa wannan tarihi ne a dalilin zurfin tunani da kuma kaifin basirarta da kuma fahimtar al’amuran duniya, duk kuwa da ƙarancin shekarunta.

Ɗalibar daga Kwalejin Nigerian Tulip International (NTIC), Rukayya, ta ɗauki hankalin alƙalan gasar da sauran jama’a saboda ƙarfin hujjojinta da ta gabatar da kuma iya bayani mai ganawarsa cikin natsuwa, lamarin da ya ba ta damar doke duk abokan karawarta.

Nafisa ta cancaci kyautar Dala 100,000 da gida da OON —Pantami NAJERIYA A YAU: Yadda Ayyuka Suka Ragu A Jihohi Bayan Kudin Shiga Ya Karu

Ita ce mutum ya biyu daga Jihar Yobe kuma daga makaranta tare da Nafisa Abdullah Aminu wadda ta zama gwarzuwa a ɓangaren Harshen Turanci a yayin gasar, inda suka wakilci Najeriya, ƙasa mai yawan al’umma sama da miliyan 200.

Nasararta nuna irin basirar da Allah Ya yi wa matasan Najeriya inda suke yin zarra a sassan duniya.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shugaban IWGA: Birnin Chengdu Zai Karbi Bakuncin Gasar Wasanni Mafi Kyau A Tarihi
  • Xizang Ya Cimma Nasarorin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Suka Kafa Tarihi Cikin Shekaru Fiye Da 60
  • Gwamnatin Yobe Za Ta Yi Taron Girmama Ɗalibar Turanci Ta Duniya, Nafisa Abdullah
  • Gwamna Aiyedatiwa Ya Bai wa Ƴar Super Falcons Tosin Demehin ₦30m Da Gida
  • Ɗaliba ’yar shekara 15 daga Yobe ta lashe Gasar Muhawara ta Duniya
  • ’Yar shekara 17 daga Yobe ta lashe Gasar Turanci ta Duniya
  • Cinikin Kamfanoni a Kasar Sin Ya Ci Gaba Da Habaka Cikin Kwanciyar Hankali A Rabin Farko Na Bana 
  • Yaran Gaza Suna Da Hakkin Rungumar Gobe
  • Gina Tituna A Karkara Yana Bunkasa Tattalin Arziki – Gwamna Sule
  • Dalilin Da Ya Sa Kashi 50 Na Ƙanana Da Matsakaitan Sana’oi Ke Durƙushewa A Nijeriya– FRC