KADSEMA da IOM sun fara tantance ɓarnar da ambaliya ta yi a Kaduna
Published: 16th, June 2025 GMT
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna (KADSEMA), tare da haɗin gwiwar Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Duniya (IOM), sun fara aikin tantance ɓarnar da ambaliya da iska suka yi a yankunan Kudancin Kaduna.
Manufar aikin ita ce su tattara sahihan bayanai daga jama’a da shugabanninsu domin a samu taimako da kuma tsara hanyoyin kare aukuwar hakan a gaba.
Yayin da suka kai ziyara Ƙaramar Hukumar Jama’a, Ko’odinetan KADSEMA na Kudancin Kaduna, Mista Ayyuka Shemang, ya ce sun fara wannan aiki ne saboda hasashen ambaliya daga Hukumar Yanayi ta Najeriya (NiMet).
Ya jaddada muhimmancin shirye-shirye tun kafin saukar daminar bana.
Shugaban tawagar IOM a Kaduna, Arhyel Mbaya, ya ce wannan aiki yana da muhimmanci don a tabbatar da cewa waɗanda ambaliya da iska suka shafa sun samu taimako yadda ya kamata.
Mataimakin Shugaban Ƙaramar Hukumar Jama’a, Emmanuel Moses Utung, ya yaba da aikin, inda ya ce sun riga sun umarci kansiloli su tattara bayanai daga mazaɓunsu.
Tawagar ta haɗa da wakilai daga Red Cross, kafafen watsa labarai, ƙungiyoyin addini, sarakunan gargajiya da jami’an gwamnati.
Waɗannan na taimakawa wajen tabbatar da cewa an gano duk wuraren da abin ya shafa.
Ana sa ran bayanan da za a samu daga wannan aiki za su taimaka wajen tsara agajin gaggawa da kuma shirye-shiryen don tunkarar sauyin yanayi a Kudancin Kaduna.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ambaliyar ruwa Barna
এছাড়াও পড়ুন:
DAGA LARABA: Dalilan al’ummomi na rungumar gwaji kafin aure
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Wasu al’ummomi sun bayyana dalilan da suka sa suka karbi tsarin yin gwajin lafiyar ma’aurata kafin a daura musu aure.
A wasu lokutan, akan samu matsaloli sakamakon rashin gwajin jini kafin a hada mace da na miji aure. Matsalolin sun hada da yaduwar cututtuka, samun ‘ya’ya marasa lafiya da sauran wasu matsalolin.
NAJERIYA A YAU: Yadda Za A Dama Da Matan Arewa A Fannin Kimiyya DAGA LARABA: Abubuwan da ya kamata yara su yi yayin hutun makarantaShirin Daga Laraba na wannan makon zai yi nazari ne kan dalilan da suka sa wasu alummomin suka rungumi yin gwajin jini kafin aure.
Domin sauke shirin, latsa nan