Tinubu Ya Kai Ziyara Benuwe Sakamakon Kisan Kiyashi Da Aka Yi Wa Jama’a
Published: 18th, June 2025 GMT
Don girmama ziyarar shugaban ƙasa, gwamnatin jihar ta ayyana ranar Laraba a matsayin hutu domin bai wa mazauna yankunan damar halarta taron da kuma bin diddigin abubuwan da suka shafi ziyarar.
Wannan ita ce ziyarar farko da Tinubu ya kai Jihar Benuwe tun bayan da rikicin ya ƙara tsananta.
Jama’a da dama na kallon wannan ziyara a matsayin gwada gwamnati kan yadda za ta shawo kan matsalolin tsaro, musamman a jihohin da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga, rikicin makiyaya da na ƙabilanci.
Kisan da aka yi a Yelwata, wanda shi ne na baya-bayan nan cikin jerin hare-haren, ya janyo suka damuwa a faɗin ƙasar tare da ƙara matsin lamba ga shugaban ƙasa da ya ɗauki matakin gaggawa don tabbatar da adalci da tsaron rayukan jama’a.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Tinubu ya tsawaita wa’adin shugaban hukumar Kwastam
Shugaba Bola Tinubu ya ƙara wa Bashir Adeniyi, Shugaban Hukumar Kwastam ta Ƙasa, karin shekara ɗaya a kan wa’adin da ya kamata ya yi na shugabancin hukumar.
Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa a ranar Alhamis.
Mutum 9 sun rasu a hatsarin kwale-kwale a Jigawa NNPCL ya sake haƙa sabbin rijiyoyin man fetur 4 a KolmaniA cewarsa, wa’adin Mista Adeniyi zai ƙare ne a ranar 31 ga watan Agusta, 2025.
Amma yanzu Shugaba Tinubu ya amince da ƙara masa shekara ɗaya, wanda hakan ke nufin zai ci gaba da zama a kan kujerarsa har zuwa watan Agustan 2026.
Sanarwar ta bayyana cewa ƙarin wa’adin zai ba shi damar kammala wasu muhimman ayyuka da yake yi.
Waɗannan ayyukan sun haɗa da gyara da inganta harkokin Kwastam, kammala wani shiri da zai sauƙaƙa kasuwanci a Najeriya, da kuma taimaka wa ƙasar wajen cika alƙawuran da ta ɗauka ƙarƙashin yarjejeniyar ciniki ta Afirka (AfCFTA).
Shugaba Tinubu, ya yaba da ƙwazon Mista Adeniyi da yadda yake gudanar da ayyukansa.
Ya ce ƙarin wannan wa’adin zai taimaka wajen inganta hanyoyin tara kuɗaɗen shiga a hukumar, da kuma tabbatar da tsaro a iyakokin Najeriya.