Amurka Ta Rufe Ofishin Jakadancinta Da Ke Tel-Aviv Na Haramtacciyar Kasar Isra’ila
Published: 16th, June 2025 GMT
Gwamnatin Amurka ta rufe Ofishin Jakadancinta da ke haramtacciyar kasar Isra’ila
Jakadan Amurka a haramtacciyar kasar Isra’ila Mike Huckabee ya sanar a yau Litinin cewa: Wani makami mai linzami na Iran ya fado kusa da ofishin jakadancin Amurka da ke birnin Tel Aviv, wanda ya yi barna kadan amma ba a samu rauni a tsakanin ma’aikatan ba.
A cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce: Daga yau Litinin ofishin jakadancin da sauran ofisoshin Amurka da suke haramtacciyar kasar Isra’ila za su ci gaba da kasancewa a rufe a matsayin matakin riga-kafi.
Jakadan ya kara da cewa: Babban abin da ya sa a gaba shi ne kare lafiyar jami’an diflomasiyyar kasarsa, kuma za su ci gaba da sanya ido kan abubuwan da ke faruwa tare da hadin gwiwar hukumomin haramtacciyar kasar Isra’ila.
উৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: haramtacciyar kasar Isra ila
এছাড়াও পড়ুন:
CMG Ta Kammala Gabatar Da Rahoto Kan Ganawar Shugabannin Sin Da Amurka
Babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin CMG, ya gabatar da labarin ganawar da aka yi jiya Alhamis tsakanin shugabannin Sin da Amurka a Busan na Korea ta Kudu, cikin harsuna 85. Kuma zuwa yau Juma’a, mutanen da suka karanta rahotanni masu alaka da ganawar ta hanyoyin watsa labarai na dandalin CMG sun kai miliyan 712. Haka kuma, kafafen watsa labarai na kasa da kasa 1678, sun wallafa tare da tura rahotanni da bidiyon labaran CMG na harsuna daban daban game da ganawar, har sau 4431.
Har ila yau a wannan rana, an gudanar taron tattaunawa na kasa da kasa kan bude kofa da kirkire kirkire da ci gaba na bai daya a kasar Uruguay, wanda CMG da hadin gwiwar ofishin jakadancin Sin dake kasar suka shirya a Montevideo babban birnin Uruguay. (Mai fassara: FMM)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA