Yafe Harajin Fito: Kasar Sin Na Cika Alkawarinta
Published: 18th, June 2025 GMT
Ta hanyar inganta manufar yafe harajin kwastam a kai a kai, kasar Sin ta samar da yanayin kasuwanci mai karko a kasashen Afirka. Bugu da kari, kasar Sin tana kallon manufofinta na rangwame a matsayin matakan tabbatar da burin samun ci gaba, inda take kokarin kyautata tsarin cinikayyar waje na kasashen Afirka, da kuma ba da goyon baya wajen raya masana’antu, da habaka tsare-tsaren tattalin arziki a Afirka.
Dalilin da ya sa kasar Sin ke kokarin tabbatar da ci gabanta da kasashen Afirka na bai daya, shi ne domin ra’ayinta game da dangantakar dake tsakaninta da Afirka, wato al’ummar Sin da Afirka suna da makomar bai daya a nan gaba. A ganin kasar Sin, ita da Afirka suna da tarihi masu kama da juna, da kuma bukatun bai daya na raya kasa. Sa’an nan, a zamanin da muke ciki, yayin da ake fuskantar sauye-sauye a fannonin siyasa, da tattalin arziki, da kimiyya da fasaha, kasashe masu tasowa na cikin wani yanayi mai wuya ta fuskar raya tattalin arzikinsu. Saboda haka, Sin da Afirka ba za su iya cimma burinsu na samun ci gaban bai daya ba, sai dai ta hanyar hadin gwiwa da juna, a bangarorin tabbatar da adalci da gaskiya a duniya , da bude kofa, da tabbatar da moriyar kowa, da kyautata muhalli, da kuma kiyaye zaman lafiya. Bisa kokarin da ake na sauya nagartaccen tunani zuwa hakikanan matakai, ko shakka babu za mu shaida karin nasarorin da Sin da Afirka za su samu, a kokarinsu na zamanantar da al’ummunsu tare. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: tabbatar da
এছাড়াও পড়ুন:
Mujallar Qiushi Za Ta Wallafi Jawabin Xi Jinping Game Da Kiyaye Muhallin Halittu
Mujallar Qiushi ta kasar Sin za ta wallafi jawabin shugaban kasar Sin Xi Jinping gobe Jumma’a 1 ga watan Agusta, wanda Xi ya taba gabatarwa a gun babban taron kiyaye muhallin halittu na kasar Sin a ranar 17 ga watan Yulin shekarar 2023.
Jawabin ya bayyana cewa, bunkasar tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasar Sin ta riga ta shiga sabon mataki na neman samun ci gaba mai inganci, wanda ke bukatar gaggauta kiyaye muhallin halittu da rage yawan iskar Carbon da ake fitarwa. Aikin kiyaye muhallin halittu na fuskantar matsin lamba. Ya kamata a yi kokarin zamanantar da kasar Sin bisa tushen samun daidaito a tsakanin bil Adama da muhallin halittu. (Kande Gao)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp