Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya bayyana cewa: Yahudawan sahayoniyya sun kashe adadi mai yawa na yaran Iran a cikin ta’addancin da suke yi 

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Ismail Baqa’i ya bayyana cewa: Gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta kashe kananan yara masu yawa na Iran a cikin wannan ta’asa da take gudanarwa kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

A cikin wani sako da Ismail Baqa’i ya rubuta a ranar Lahadin da ta gabata ya bayyana cewa: “Gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta kashe adadi mai yawa na yara Iraniyawa tare da kai hari kan asibitin yara a tsawon kwanaki uku na hare-haren soji kan Iran. Kamar yadda Ya’ir Golan, tsohon mataimakin hafsan hafsoshin sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila ya amince da cewa: Kashe yara wani nau’i ne na nishaɗi a gare su.”

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami

A wani bidiyo daban da PUNCH Metro ta gani a Facebook, wanda Mc Pee ya wallafa, wani mutum da ake zargin dalibi ne na jami’ar ya bayyana abin da ya faru.

A cewarsa, marigayin ya roki a bar shi ya rayu kafin daga bisani wanda ake zargin ya kashe shi.

Ya ce: “Nanpon ya riga ya yanke Peter a kumatunsa yayin da yake rokon a bar shi. Lokacin da muka shiga tsakani muka ce ya daina, sai ya yi barazanar yanka duk wanda ya kusanto shi.

“Da Peter ya ga ba ya sauraron rokonsa, sai ya rungume shi yana rokonsa da kuka.

“Mun fita neman taimako amma babu wanda ya amsa mana. Da Peter ya yi kokarin tserewa sai ya fadi, Nanpon ya kamo shi ya ci gaba da saransa da adda.”

Wani kwararren masanin tsaro da yaki da ta’addanci ya wallafa a dandalin D a ranar Lahadi cewa jami’an rundunar ‘yan sandan Jihar Filato sun kama wanda ake zargin.

Ya kuma ambaci majiyoyi da suka tabbatar da faruwar lamarin ta hanyar rahoton da aka samu daga Babban Jami’in Tsaro na jami’ar.

Ya rubuta cewa, “Rundunar ‘Yansanda ta Filato ta kama wani dalibi mai shekaru 23 na Jami’ar Jos bisa zargin kashe abokinsa sannan ya binne shi a rami mara zurfi a cikin dakinsa da ke kauyen Rusau a Karamar Hukumar Jos ta Arewa.

“Majiyoyi sun tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadi a Jos, inda suka danganta da rahoton da aka samu daga Babban Jami’in Tsaron jami’ar.

“A cewar majiyoyin, wanda ake zargin mai suna Dabid Nanpon Timmap, dalibi a matakin shekara ta uku a jami’ar, ya kai wa Peter Mata Mafurai, mai shekaru 22, hari da adda, ya kashe shi a gidansa.”

Zagazola ya kara da cewa, bayan samun kiran gaggawa da misalin karfe 9:30 na safiya, DPO na sashin Laranto ya jagoranci tawagar ‘yansanda zuwa wurin, inda aka kama wanda ake zargin.

“Majiyoyin sun ce bincike ya nuna cewa wanda ake zargin ya binne mamacin a cikin rami mara zurfi da ya haka a cikin dakinsa. An tono gawar kuma an kai ta dakin ajiye gawarwaki na Asibitin koyarwa na Jami’ar Bingham domin yin binciken gawar (autopsy),” in ji shi.

Ya kara da cewa, an tsare wanda ake zargin yayin da ake ci gaba da bincike domin gano hakikanin dalilin kashe abokin nasa.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sojoji Sun Kama Ƴan Ta’adda 20, Sun Ceto Mutane 17 Da Aka Yi Garkuwa Da Su November 1, 2025 Manyan Labarai Gwamnatin Tarayya Ta Mayar Da Martani Kan Iƙirarin Trump Na Kisan Ƙare Dangi Ga Kiristoci November 1, 2025 Manyan Labarai Shugabar Tanzania Samia Suluhu Ta Lashe Zaɓe, Duk Da Rikicin Da Ya Mamaye Ƙasar November 1, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Wasu Yan Ta’adda Sun Kashe Dakarun Sa Kai 2 A Kudu Maso Gabashin Iran
  • Isra’ila Ta Kashe Mutane 4 Tare Da Jikkata Wasu Guda 3 A Kudancin Labanon
  • Iran Ta Gargadi Isra’ila Kuma Tasha Alwashin Kare Shirinta Na Nukiliya
  • Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya
  • Dalibin Jami’ar Jos Ya Kashe Abokinsa Ya Binne Gawar A Rami
  • ‘An Kashe Masu Zanga-zanga Akalla 500 a Tanzania’
  • An Cafke Ma’aikatan Gidan Marayu Da Suka Sayar Da Yara 4 A Kan Naira Miliyan 3
  • Ranar Foliyo Ta Duniya: Muna Fatan Ganin Karshen Cutar Foliyo A Jihar Katsina -Zulaihat Dikko Radda
  • An Yi Wa Yara Sama Da Miliyan Biyu Allurar Rigakafin Mashaƙo Da Sankarau A Zamfara
  • Gaza: hare-haren Isra’ila sun kashe mutane 100 Cikin Kwanaki Biyu