Jirgin alhazai ya yi saukar gaggawa kan barazanar harin bom
Published: 17th, June 2025 GMT
Alhazai 442 sun tsallake rijiya da baya, bayan jirgin da ya ɗauko su bayan sun kammala aikin Hajjin bana ya samu sakon cewa an dasa bom a cikinsa a yayin da yake sararin samaniya a ƙasa Indonesiya.
A ranar Talata ne jirgin, mallakin kamfanin Saudia Air, ya yi saukar gaggawa a birnin Jakarta babban birnin ƙasar Indonesiya, bayan da ya ɗauko alhazan da daga birnin Jidda na ƙasar Saudiyya.
’Yan sanda ƙasar Indonesiya sun ce an yi nasarar fitar da ɗauƙacin fasinjojin jirgin su 442 a filin jirgi da ke lardin Sumatra ta Arewa.
Ma’aikatar Sufuri ta ƙasar Indonesiya ta ce jirgin ya yi saukar gaggawa ne bayan samun wani saƙon imel cewa an sanya bom a jirgi.
Sarki ya yi barazanar hana yin Musulunci a garinsa bayan dodanni sun kai wa Musulmi hari Matatar man Isra’ila ta daina aiki bayan sabon harin IranTa bayyana cewa bayan kwashe mutanen, ’yan sanda sun fara aikin bincike domin gano bom ɗin da kuma lalata shi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Indonesiya Saudiyya saukar gaggawa
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan Najeriya miliyan 34 na cikin barazanar yunwa
Akalla ’yan gudun hijira miliyan daya da dubu 400 da ke Arewa maso gabashin Najeriya ne suke fuskantar barazanar yunwa bayan yanje tallafin da Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ke bayarwa.
Wani rahoton majalisar a kan abinci da tsaro wanda gwamnatin Najeriya, Shirin Kula da Abinci na Majalisar (FAO) da sauran masu ruwa da tsaki a baya dai sun yi hasashen ’yan Najeriya miliyan 33.1 za su iya fuskantar matsanancin karancin abinci daga tsakanin watan Yuni zuwa Agustan 2025.
Mun ci ribar Naira biliyan 414 a cikin wata 6 a Najeriya – Kamfanin MTN Za a kashe biliyan 712.26 don yi wa filin jirgin saman Legas garanbawulHakan dai na nufin a yanzu yan kasar miliyan 34.7 ne ke nan suke cikin barazanar yunwar.
Ofishin Majalisar mai kula da Agaji (UNOCHA), a rahotonsa na mai taken “Najeriya a 2025 bukatun agajinta da kuma hanyoyin magance su” ya yi bayani daki-daki kan kalubalen da ake fuskanta a jihohin Adamawa da Borno da kuma Yobe.
Rahoton ya ce akwai akalla yara miliyan daya da dubu 800 da kef ama da matsanancin karancin abinci.
Rahoton ya alakanta hakan da ci gaba da karuwar farashin kayayyaki a Najeriya wanda ya kai kaso 40.9 cikin 100 a watan Yunin 2024.
Kazalika, karuwar adadin na da nasaba da rage tallafin da MDD ke bayarwa ba, sanadiyyar yanke mata kudaden tallafin da musamman Amurka ke bayarwa.