Motoci Masu Aiki Da Lantarki Kirar Sin Sun Samar Da Sabuwar Hanyar Sufuri Ga Al’Ummun Kasashen Shiyyar Tsakiyar Asiya
Published: 19th, June 2025 GMT
A watan Afrilun bana, wata farar mota kirar bas mai tsawo mita 12, ta yi tafiya a kan titunan Ashgabat, hedkwatar kasar Turkmenistan. Bas din da kamfanin Yutong na kasar Sin ya kera ta dace da ma’aunin kiyaye muhalli da kasar ta tanada, kuma tana dauke da na’urar ba da jagorancin sufuri mai amfani da tauraron dan Adam, da na’urar biyan kudi ta yanar gizo, matakin da ya bullo da sabuwar hanyar zirga-zirga ga jama’ar wurin.
A wannan shekara, Sin za ta samar da irin wannan bas har 700 ga Ashgabat, matakin da zai biya bukatun zirga-zirgar jama’ar kasar da yawansu ya zarce miliyan 1.
Tun da aka bude taron koli na Sin da kasashen shiyyar tsakiyar Asiya karon farko a shekarar 2023, Sin da kasashen shiyyar Asiya, sun rika bullo da boyayyen karfin hadin gwiwarsu, sun kuma cimma nasarar fitar da sabuwar hanyar hada hannu ba tare da gurbata muhalli ba.
Daga cikin bangarorin hadin gwiwarsu, sana’ar kera motoci na kan gaba. Kamfanonin Sin da dama sun kafa sassansu a wuri, matakin da ya zurfafa hadin gwiwarsu, da samarwa jama’ar wurin wata sabuwar hanyar zirga-zirga, har ma ya samar da karin guraben aikin yi, da karawa jama’ar wurin kudin shiga, kana da horar da ma’aikata a wannan sana’a, matakin da ya kara bunkasa kwarewarsu. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Babban Jirgin Ruwan Kasar Sin Ya Nufi Yankin Tekun Kudancin Kasar Domin Gwaji Da Samar Da Horo
Kakakin ma’aikatar tsaron kasar Sin Jiang Bin, ya ce a baya bayan nan babban jirgin ruwan dakon jiragen sama na kasar Sin mai suna Fujian, ya doshi yankin tekun kudancin kasar, inda ya ratsa ta zirin Taiwan, a kan hanyarsa ta gudanar da gwaje-gwaje da samar da horo.
Jami’in wanda ya bayyana hakan a Talatar nan, ya ce hakan bangare ne na ayyukan da aka saba gudanarwa lokaci-lokaci a wani bangare na kirar jirgin.
Jiang Bin, ya yi tsokacin ne yayin da yake amsa wata tambaya mai nasaba da hakan da aka yi masa, yana mai cewa, bulaguron jirgin ya dace da dokokin kasa da kasa da ayyuka masu nasaba, kuma ba shi da wata nasaba da tunkarar wani sashe. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp