Aminiya:
2025-11-03@06:53:40 GMT

Matatar man Isra’ila ta daina aiki bayan sabon harin Iran

Published: 17th, June 2025 GMT

Hukumar gudanarwar matatar man ƙasar Isra’ila da ke yankin Haifa ta sanar cewa matatar ta dakatar da ayyukanta ɗungurungum bayan harin da Iran ta kai mata.

Kamfanin Bazan Group da ke kula da matatar ya ce harin na Iran ya tilasta musu tsayar da gaba ɗaya — a yayin da sabon rikicin na yankin Gabas ta Tsakiya ke ɗaukar zafi tsakanin ƙasashen biyu da suka jima suna yi wa juna kallon hadarin kaji.

Bazan Group ya bayyana harin rokokin Iran ya lalata tashar wutar lantarki da matatar ke amfani da shi.

Harin na Iran ya kuma halaka ma’aikata uku a matatar ta Haifa, kamar yadda hukumomin Isra’ila suka sanar.

Wannan na faruwa a ci gaba hare-haren ramuwar gayya da makamai masu linzami da Iran ke kaiwa, bayan jiragen Isra’ila sun ƙaddamar da hare-hare da kawo yanzu suka yi ajalin mutane sama da 220 a sassan Iran, har da Tehran, Babban birnin ƙasar.

Kashi 70 na mutanen da Isra’ila ta kashe a Iran da mata da ƙananan yara ne; da wasu manyan jami’an tsaro da wani masanin kimiyyar makamashin nukiliya.

Aminiya ta ruwaito Isra’ila na cewa ta ƙaddamar da hare-haren ne domin daƙile Iran, wadda ke dab da mallakar makamin nukiliya a cikin wannan shekara, ko cikin watanni kaɗan masu zuwa.

Ana iya tuna cewa Fira Minista Banjamin Netanyahu ya bayyana cewa hallaka shugaban addinin Iran, Ayatullah Alkhamene’i zai yi tasiri wajen kawo karshen ta’addnacin Iran.

A nata bangaren Iran ta Bayyana cewa Isra’ila za ta yaba wa aya zaƙi, kan waɗannan hare-haren ragoncin da ta kai wa fararen hula da cibiyoyin soji da tashoshin makamashin nukiliyarta.

Ta kuma bayyana harin bai tsayar da shirinta na nukiliya domin Samar da wata lantarki da sauran abubuwa na zaman lafiya ba.

Ramuwar gayyar Iran ta shafi cibiyoyin sojin Isra’ila da tashar wutar lantarki da matatar mai, baya ga halaka mutane sama da 24 da lalata gine-gine a wurare daban-daban, ciki har da birnin Kudus, da kuma Tel Aviv, babban birnin ƙasar Isra’ila.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Gabas ta Tsakiya hare hare Iran Isra ila Matatar mai nukiliya

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Jigawa Ta Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda

Daga Usman Muhammad Zaria

 

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta yi kira ga mazauna jihar Jigawa da su kasance masu bin doka da oda, tare da yin aiki kafada da kafada da rundunar ‘yan sanda domin tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a fadin jihar.

Kwamishinan ‘Yan Sanda na jihar Jigawa, CP Dahiru Muhammad, ne ya bayyana haka lokacin da ya karɓi sabbin motoci 10 kirar Toyota Hilux da Gwamna Umar Namadi ya bai wa rundunar a Dutse, babban birnin jihar.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, SP Lawan Shiisu Adam, ya fitar, CP Dahiru Muhammad ya yaba da jajircewar Gwamna Umar Namadi wajen tallafa wa hukumomin tsaro domin sauke nauyin da ke kansu a jihar.

Ya bayyana cewa, wannan gudummawa ta nuna cikakken kudirin gwamnatin Gwamna Namadi na ƙara inganta harkokin tsaro da kuma tallafawa Rundunar ‘Yan Sanda ta Najeriya wajen aiwatar da aikinta na kare rayuka da dukiyoyin jama’a a fadin jihar.

Kwamishinan ya nuna cewa, waɗannan sabbin motoci 10 za su taimaka matuƙa wajen rage lokacin da ake ɗauka kafin amsa kiran gaggawa, tare da ƙara inganta aikin rundunar a fadin jihar.

Ya ƙara da cewa, za a yi amfani da motocin yadda ya kamata, tare da kula da su don tabbatar da ingantaccen  tsaro.

CP Dahiru Muhammad ya kuma sake jaddada aniyar rundunar wajen ci gaba da tabbatar da zaman lafiya, doka da oda, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Al’ummar Kauru Sun Koka Game Da Karuwar Hare-hare Da Ke Barazana Ga Gonaki Da Rayuka
  • Ziyarar Shugaba Xi A Koriya Ta Kudu Ta Bude Babin Yaukaka Hadin Gwiwar Yankin Asiya Da Fasifik
  • Taron APEC Na 2026 Da Za A Shirya A Kasar Sin Zai Bude Sabon Babin Na Gina Al’ummar Bai Daya Ta Asiya-Pasifik
  • An Bude Sabon Babin Huldar Sin Da Koriya Ta Kudu
  • Araqchi: Da Hadin Bakin Amurka, Gwamnatin Isra’ila ta kaddamar Da Hari Kan Kasar Iran
  • Iran Ta Gargadi Isra’ila Kuma Tasha Alwashin Kare Shirinta Na Nukiliya
  • Gwamna Uba Sani Ya Bayyana Tsare-tsaren Ci Gaban Kaduna a Taron Duniya a Dubai.
  • Gwamna Namadi Ya Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda
  • Gwamnatin Jigawa Ta Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Gina Gidaje 52 A Babban Birnin Jihar