Leadership News Hausa:
2025-08-09@09:27:11 GMT

Sin Ta Cimma Sabuwar Nasarar Bincike Duniyar Wata

Published: 18th, June 2025 GMT

Sin Ta Cimma Sabuwar Nasarar Bincike Duniyar Wata

Kasar Sin ta cimma nasarar aikin gwajin tserewa lokacin da ake gamu da matsala a matakin farko na harbar kumbo mai dauke da mutane na “Mengzhou” a yau Talata, a cibiyar harbar taurori dan Adam dake birnin Jiuqiu, abin da ya alamanta cewa, Sin ta cimma sabuwar nasara a aikin binciken duniyar wata tare da kumbo mai daukar mutane.

Wannan ita ce nasara irinta ta biyu da Sin ta samu a wannan bangare, bayan shekaru 27 da suka gabata, da samun nasara ta farko a aikin gwajin da ta gudanar a shekarar 1998.

Aikin gwajin tserewar da aka gudanar ya kasance muhimmin mataki na ba da tabbaci ga rayukan ’yan saman jannati, wato idan an gamu da hadari ko matsala ba zato ba tsammani, za a iya samar da jagoranci ga sashen kumbo mai dawowa ya bar wuri ma hadari, tare da dawo da ’yan saman jannati doron duniyarmu lami lafiya.

Kumbo mai daukar mutane na “Mengzhou”, sabuwar na’ura ce da Sin ta kera bisa dogaro da karfin kashin kanta, da zummar gudanar da nazarin sararin samaniya a nan gaba lami lafiya, wanda ke iya tashi zuwa sararin samaniya da dawowa doron kasa, wannan kumbo mai iya daukar mutane 7 na kunshe da fasaha ta sahun gaba a duniya. (Amina Xu)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Kwamitin Sulhu na MDD na Shirin gudanar da zaman gaggawa kan batun Gaza

A gobe Lahadi ne kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai gudanar da wani zaman gaggawa kan halin da ake ciki a zirin Gaza, kamar yadda wakilin Al-Mayadeen a birnin New York ya bayyana.

Wannan shawarar ta zo ne bayan amincewar majalisar ministocin Isra’ila da shirin firaministan Haramtacciyar Kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu, wanda ya hada da shirye-shiryen sojojin Isra’ila na mallake birnin Gaza.

Shirin ya tanadi wasu ka’idoji guda biyar na kawo karshen yakin, wanda ya fara da “kwace makaman Hamas,” sannan a dawo da dukkan fursunonin wadanda ke raye ko a mace.

Hakan zai biyo bayan kwance damarar zirin Gaza gaba daya, da kafa wata sabuwar gwamnatin da ba ta karkashin ikon kungiyar Hamas ko kuma hukumar Falasdinawa.

Za a gudanar da zaman gaggawa na kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a daidai lokacin da mamayar Isra’ila ke ci gaba a a cikin yankunan Gaza, gami da kai munanan hare-hare babu kakakutawa tsawon kusan shekaru biyu a jere, lamarin da ya jefa fararen hula sama miliyan biyu a cikin mawuyacin hali da kunci, baya ga matakan baya-bayan nan nah ana shigar da abinci da kayayakin buatar rayuwa zuwa yankin wanda Isra’ila take aiwatarwa, wanda shi ma ya  haifar da matsananciyar yunwa a a yankin zirin Gaza baki daya.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran da Masar sun jaddada wajabcin daukar matakan kawo karshen kisan kiyashi a Gaza August 9, 2025 Jamus ta dakatar da ba wa Isra’ila kayayyakin aikin soji saboda shirinta na mamaye Gaza August 9, 2025 Hizbullah: Amurka na hakoron taimaka wa ajandar Isra’ila ne a kan Lebanon August 9, 2025 Ramaphosa da Putin sun tattauna rikicin Ukraine da batutuwan da suka shafi kasashensu August 8, 2025 Australia ta gargadi Isra’ila game da yunkurin mamaye Gaza August 8, 2025 Axios: Majalisar ministocin Isra’ila ta amince da sabon shiri na mamaye birnin Gaza August 8, 2025 Iran Ta Kira taron Gaggawa Na Kungiyar Kasashen Musulmi August 8, 2025 Iraniyawa Miliyon 1.2 Ne Suka Shiga Iraki Ta Kofar Shiga Na Mehran August 8, 2025 Ansarullah Ta Yi Gargadi Ga Amurka Da HKI Kan Kara Tada Hankali A Yakin August 8, 2025 Hizbullah Da Amal Sun Yi Tir da Shirin Kwance Damarar Hizbullah August 8, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Kwamitin Sulhu na MDD na Shirin gudanar da zaman gaggawa kan batun Gaza
  • Iran da Masar sun jaddada wajabcin daukar matakan kawo karshen kisan kiyashi a Gaza
  • Xi Ya Bukaci A Yi Dukkan Mai Yiwuwa Wajen Gudanar Da Ayyukan Bincike Da Ceto Bayan Aukuwar Ambaliya A Lardin Gansu
  • Jirgin Daukar Marasa Lafiya Ya fadi A kasar kenya Ya Kuma Kashe Akalla mutane 6
  • Kasar Sin Ta Kammala Gwajin Farko Na Sauka Da Tashin Kumbon Binciken Duniyar Wata Mai Dauke Da Bil Adama
  • An Biya Diyyar Naira Miliyan 277 Ga Wadanda Aikin Ginin Masallacin Gumel Ya Shafa
  • Araqchi: Ba a kayyade wani lokacin shiga wata sabuwar tattaunawa da Amurka ba
  • Majalisa ta buƙaci ƙirƙirar sabbin ƙananan hukumomi a Bauchi
  • Tinubu Ya Taya Nafisa, Rukayya, Hadiza Murnar Samun Nasarar Zama Gwanaye A Gasar Turanci Ta Duniya
  • Jami’an Alhazai Sun Karrama DG Labbo Bisa Nasarar Hajjin 2025