Gwamna Namadi Ya Dage Dakatarwar Da Aka Yi Wa Mai Bashi Shawara Na Musamman
Published: 6th, March 2025 GMT
Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya dage dakatarwar da aka yi wa mai bashi shawara na musamman kan harkokin albashi da fansho, Bashir Ado Kazaure da aka mishi a baya ba tare da bata lokaci ba.
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Jigawa Malam Bala Ibrahim ya sanyawa hannu kuma ya bai wa manema labarai.
Sanarwar ta bayyana cewa, matakin na zuwa ne bayan wani kwakkwaran bincike da kwamitin da aka kafa karkashin jagorancin babban lauyan gwamnati kuma kwamishinan shari’a na jihar Barista Bello Abdulkadir Fanini ya gudanar.
“Rahoton kwamitin ya yi tsokaci kan al’amuran da suka dabaibaye dakatarwar da aka yi wa Bashir Kazaure, biyo bayan sanarwar batun biyan mafi karancin albashi na Naira 70,000 kafin lokacin da gwamnati ta shirya sanarwa a hukumance,” in ji shi.
Sakataren gwamnatin jihar ya bayyana cewa, matakin dage dakatarwar na nuni da yadda Gwamnan ya jajirce wajen tabbatar da adalci da bin doka da oda wajen tafiyar da al’amura.
Usman Muhammad Zaria
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Na Da Kwamitoci 30 Da Ke Sa Ido Kan Ma’aikatun Gwamnati
Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta ce akwai kwamitoci guda 30 da aka daurawa nauyin bibiyar yadda ma’aikatu da hukumomin gwamnatin Jihar ke sarrafa kudade domin gudanar da harkokin yau da kullum, gami da ayyukan raya kasa.
Shugaban Kwamatin kananan hukumomi na majalisar dokokin jihar, Alhaji Aminu Zakari, ya bayyana hakan lokacin wata ziyarar aiki a karamar hukumar Babura.
Yayi bayanin cewar, an dorawa Kwamatinsa alhakin duba kananan hukumomi domin tabbatar da shugabanci nagari a yankunan karkara.
A cewarsa, kwamatin yana duba kundin bayanan sha’anin mulki da na harkokin kudi da suka hada da jadawalin kudaden da karamar hukuma ke samu daga kason arzikin kasa, da littafin hulda da banki,da takardun biyan kudade na voucher da kundin bayanan tarukan kwamitocin karamar hukuma domin tabbatar da ritita kudaden gwamnati.
Alhaji Aminu Zakari ya kuma lura cewar, ziyarar tana bada damar ganawa tsakanin ‘yan kwamatin da masu ruwa da tsaki na kananan hukumomi domin tattaunawa da su, da nufin samar da kyakkyawan yanayin aiki tare tsakanin bangarori daban daban.
Karamin Kwamatin da wakilin mazabar Guri Alhaji Usman Abdullahi Tura Musari ya jagoranta, ya duba aikin noman shinkafa a fadamar Garu da ta Dangoriba da karamar hukumar Babura ta bullo da shi akan Kudi Naira Milyan 49 da dubu 500, inda aka samar da rijiyoyin ban ruwa dari-dari a kowacce fadama.
Alhaji Usman Musari ya kuma yabawa karamar hukumar Babura bisa kyakkyawar aniyarta, ta mara baya ga kokarin gwamnatin Malam Umar Namadi wajen bunkasa tattalin arzikin matasa ta fuskar hadahadar aikin noma.
A jawabin sa, shugaban karamar hukumar Babura Malam Hamisu Muhammad Garu, ya bayyana ziyarar a matsayin wani sanannen aiki da Majalisa ke yi duk shekara, inda ya yi kira ga ma’aikata da ‘yan majalisar zartaswar karamar hukumar da su bada cikakken hadin kai domin samun nasarar ziyarar.
Sauran ‘yan kwamatin sun hada da mataimakin shugaban kwamatin kuma wakilin mazabar Kaugama Alhaji Sani Sale Zaburan da wakilin mazabar Kanya Babba Alhaji Ibrahim Hashim Kanya da mataimakan sakatare da Oditoci biyu.
Usman Mohammed Zaria