Wani Matashi Ya Ƙone Kansa A Kano Saboda Yana Son Zuwa Aljanna
Published: 18th, June 2025 GMT
“Da farko mun ɗauka yana wasa ne, amma kafin wani ya kai ɗauki, ya riga ya kunna wa kansa wuta.”
Wata mazauniyar yankin, Aisha Salisu, ta ce yana matashin yana shaye-shaye.
“Ba ya cikin hayyacinsa. Ana jin warin wani abu mai ƙarfi a jikinsa, kuma yana karkarwa da ihu,” in ji ta.
Mutane sun yi ƙoƙarin taimaka masa.
Wasu sun ja shi zuwa cikin ruwan da ke wata magudanar ruwa a gefen hanya, amma wutar ta riga ta yi masa ƙone sa.
“Abun ya zama kamar fim kuma mai ban tsoro,” in ji wani direban adaidaita sahu mai suna Ibrahim Jafar.
“Ko bayan da suka jefa shi cikin ruwan, wutar ba ta daina ci nan take ba. Fatar jikinsa duk ta ɗaye.”
Hukumomi ba su fitar da wata sanarwa ba tukuna dangane da lamarin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Panshekara Shaye Shaye
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu ya karɓi baƙuncin Abdulmumin Jibrin Kofa
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karɓi baƙuncin ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Kiru da Bebeji na Jihar Kano, Abdulmumin Jibrin Kofa.
Aminiya ta ruwaito cewa Kofa, wanda makusanci ne ga jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, kuma ɗaya daga cikin jiga-jigai a jam’iyyar NNPP, ya ziyarci shugaban ƙasar ne a yau Laraba.
Za a kammala shimfiɗa layin dogo daga Kaduna zuwa Kano a 2026 — Gwamnatin Tarayya Tattalin arzikin Nijeriya zai ci gaba da bunƙasa har zuwa baɗi — IMFHar yanzu dai babu wasu bayanai dangane da abin da suka tattauna, amma ziyarar wadda hadimai daga ɓangarorin biyu suka riƙa yaɗawa na ci gaba da ɗaukar hankalin jama’a.