Leadership News Hausa:
2025-08-02@02:46:15 GMT

Masu Karanta Adabin Shafin Intanet Na Sin Sun Kai Miliyan 575

Published: 17th, June 2025 GMT

Masu Karanta Adabin Shafin Intanet Na Sin Sun Kai Miliyan 575

Yawan masu karanta adabin da aka dora a shafin intanet na kasar Sin ya karu zuwa miliyan 575, lamarin da ya nuna yadda ake samun karuwar karanta labarai da rubutun zube ta fasahar zamani a fannin al’adun kasar.

Masu karatu da aka haifa bayan shekarar 2000 su ne suka kara yawan ci gaban da aka samu a baya-bayan nan, wadanda suka dauki kusan kashi hudu na dukkan masu karatu a shafin na intanet, kamar yadda wani rahoto da kungiyar marubuta ta kasar Sin ta fitar a yau Talata ya bayyana.

Bisa bayanan da aka samu daga manyan dandalolin adabi na intanet guda 50 a fadin kasar Sin, rahoton ya kiyasta cewa, masana’antar adabin ta samar da kudin shiga kusan yuan biliyan 44, kimanin dalar Amurka biliyan 6.1 a shekarar 2024. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Binciken CGTN: Za A Ci Gaba Da Nuna Kyakkyawan Fata Ga Bunkasar Sin Nan Da Shekaru 5

Bayanin da ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS ya yi a baya-bayan nan game da hasashe kan tattalin arzikin kasar Sin cikin shekaru biyar masu zuwa ya jawo hankalin duniya sosai. Kuma sakamkon binciken jin ra’ayoyin jama’a da CGTN na babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG ya yi a tsakanin masu bayyana ra’ayoyi 47,000 a kasashe 46 daga shekarar 2023 zuwa 2025, ya nuna jama’ar sun nuna yakini game da karfi da juriyar tattalin arzikin kasar Sin.

Binciken ya nuna cewa, yawancin masu bayyana ra’ayoyin daga sassan duniya suna da kyakkyawan fata ga tattalin arzikin kasar Sin wajen samun bunkasa mai kyau a dogon lokaci, inda amincewarsu ta kai kashi 74.7 bisa dari, da 81.3 bisa dari, da kuma 81.9 bisa dari cikin shekaru uku a jere.

Binciken da aka yi a bana ya kuma nuna cewa, masu bayyana ra’ayoyin suna da kwarin gwiwa game da samun damammaki masu kyau a kasuwar Sin a cikin yanayin kasa da kasa mai sarkakiya da tashe-tashen hankula. A cikinsu akwai kashi 79.8 bisa dari da suka bayyana cewa, babbar kasuwar Sin ta ba da muhimman damammaki ga kasashen da suke gudanar da kasuwanci a ciki.(Safiyah Ma)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An ceto mutum uku da aka yi garkuwa da su a Kebbi
  • NBRDA Za Ta Hada Gwiwa Da KIRCT Domin Habaka Magunguna Da Yaki Da Cututtuka
  • Nijeriya Na Asarar Kusan Naira Tiriliyan 17.9 Duk Shekara Sakamakon Cutar Hanta — Gwamnati
  • Karamar Hukumar Birnin Kudu Ta Shirya Taron Bita Ga Kansiloli
  • Habasha Ta Kaddamar Da Shirin Shuka Bishiyoyi Miliyan 700 A Rana Daya
  • INEC Ta Gudanar da Taron Masu Ruwa da Tsaki Kafin Zaɓen Cike Gurbi na Babura/Garki
  • Samar da makamashi mai tsafta na zamani shi ne fatanmu — Guterres
  • Binciken CGTN: Za A Ci Gaba Da Nuna Kyakkyawan Fata Ga Bunkasar Sin Nan Da Shekaru 5
  • Manyan makarantu 2 ne kacal ke da rajista a Katsina — Gwamnati
  • An Kaddamar da Makon MNCH na 2025, Ya Rarraba Fakitin Bayarwa 6,000, Kayan C/S 500