2025 UTME: Cibiyoyin Zana Jarabawar 11 Na Fuskantar Barazanar Dakatarwa – JAMB
Published: 17th, June 2025 GMT
Ga cibiyoyin CBT, Oloyede ya ce dole ne a gargadi wadanda ke da hannu sannan a nemi su sanya hannu kan takardar yarjejeniya. Kuma bayan yarjejeniyar, za a kuma buƙaci su ba da shaidar horar da masu rajistar daliban.
Da yake karin haske kan shawarwarin, Oloyede ya ce hukumar ba za ta yi la’akari da duk wani uzuri ba daga cibiyoyin da abin ya shafa a nan gaba ba, duk da ikirarin da suke yi na rashin sani, don haka akwai bukatar su samu horon da ya dace a jami’o’in gwamnatin tarayya da ke kusa da su kafin JAMB ta kara amincewa da su.
Cibiyoyin CBT da abin ya shafa da aka gayyata taron sun hada da Misau Emirate ICT Centre, Misau, Bauchi, Ijaw National Academy, Kiama, Bayelsa, Directorate of ICT Nigerian Army University, Biu, Gombe, Emerald IT Academy Limited, Benin, Tigh Technologies, Sascon International School, Maitama, Abuja, Jicoras CBT Centre, Babura, Jigawa da Huntsville Technology Limited, Anthony, Legas
Sauran sun hada da Jolas College CBT Centre, Obalende, Lagos, Abdul Ocean Weath CBT Centre, Ibadan, Oyo State, National Open University of Nigeria (NOUN), Wase, Filato da Consulate Salle D’Examen CBT Centre, daura da Jonny Lane/Navy Barrack Agip Estate, Jihar Ribas.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Mun ci ribar Naira biliyan 414 a cikin wata 6 a Najeriya – Kamfanin MTN
Kamfanin sadarwa na MTN ya sanar da cin ribar Naira biliyan 414 a watanni shida na farkon shekarar 2025 a Najeriya.
Kamfanin ya bayyana hakan ne a rahotonsa na karshen wata shidan da ya gabatar a gaban Hukumar da ke Kula da Kasuwar Hannun Jari ta Najeriya a ranar Alhamis.
Za a kashe biliyan 712.26 don yi wa filin jirgin saman Legas garanbawul NAJERIYA A YAU: Me dokar kasa ta ce kan karin wa’adin aiki da Shugaban Kasa ke yi?A cewar rahoton, kamfanin ya kuma tafka asarar da ta kai ta Naira biliyan 90 saboda musayar kudaden kasashen waje.
Rahoton ya kuma ce jimillar abin da kamfanin ya samu a tsawon lokacin kafin a cire riba ya kai Naira tiriliyan daya da biliyan 200.
Kazalika, MTN ya ce kudaden shigar da ya samu daga kiran waya a watannin sun kai biliyan 887, yayin da na data kuma suka kai tiriliyan 1.23.
Kamfanin dai ya alakanta nasarorin da ya samu da ingantuwar yanayin kasuwanci a Najeriya, ciki har da daidaita farashin Naira da kuma saukar farashin kayayyaki.