Litar fetur za ta iya komawa N1,000 a Najeriya saboda yakin Isra’ila-Iran – Masana
Published: 18th, June 2025 GMT
Masana sun yi gargadin cewa yakin da ake gwabzawa a tsakanin Isra’ila da Iran zai iya shafar farashin man fetur a duniya kuma hakan zai iya yin illa ga tattalin arzikin Najeriya.
Masanan na cibiyar Commercio Partners da ke Legas sun bayyana fargabar ce a cikin wani rahoto da cibiyar ta fitar mai taken: “Farashin kayayyaki ya sauka a Najeriya a watan Mayu, amma akwai matsala a nan gaba” wanda aka wallafa shi ranar 16 ga watan Yunin 2025.
A cewar rahoton, rikicin da ake fama da shi a yankin Gabas ta Tsakiya zai iya rage yawan man fetur din da ake samarwa a duniya wanda kuma zai kai ga tashin farashinsa a kasuwanni.
Ma’aikatan Kwalejin Ilimi ta jihar Kaduna za su tsunduma yajin aiki Ambaliyar Mokwa – Har yanzu muna neman mutum 700 – Gwamnatin NejaSun yi gargadin cewa duk da yake Najeriya kasa ce mai arzikin man na fetur, amma tashin farashin ba lallai ne ya zama alheri ga kasar ba.
Aminiya ta rawaito cewa farashin danyen mai ya rika yin tashin gwauron zabo a ’yan kwanakin nan inda ya haura Dalar Amurka 75 kan kowacce ganga.
Sai dai tashin na nufin farashinsa zai tashi a gida Najeriya, inda farashin zai iya kaiwa Naira 1,000.
A yanzu dai ana sayar da man ne daga tsakanin N870 zuwa N920 a gidajen mai.
“A Najeriya kuwa, inda yanzu aka janye tallafin man fetur kuma farashinsa ya ta’allaka da kasuwar duniya, hakan zai iya shafar tattalin arzikin kasar,” in ji masanan.
Rahoton ya kuma ce duk da cewa matatar mai ta Damngote na aiki, duk da haka kasar ba ta tsira daga barazanar ba.
Ya kuma ce, “Har yanzu shigo da mai ake zuwa Najeriya, kuma tashin farashinsa a kasuwannin duniya na nufin yadda ake tace shi da rarrabawa ko dakon shi su ma za su karu
“Idan danyen man ya kara tsada, farashin man fetur a Najeriya – wanda yanzu haka yake wajen N825 – zai iya komawa kusan N1,000,” kamar yadda masanan suka yi hasashe.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Iran Isra ila Najeriya
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Tarayya Za Ta Kwaso ‘Yan Nijeriya Da Suka Maƙale A Isra’ila Da Iran
Sanarwar ta ƙara da cewa ana aiki tare da hukumomin cikin gida da na ƙasa da ƙasa domin ganin an gudanar da aikin kwasar cikin tsaro.
Sanarwar ta ce: “Ma’aikatar Harkokin Waje na sanar da jama’a cewa, sakamakon rikicin da ke ƙara ƙamari tsakanin Isra’ila da Iran, Gwamnatin Tarayya tana shirin ƙarshe na kwaso ‘yan Nijeriya da suka maƙale a waɗannan ƙasashe.
“Saboda haka, ana shawartar dukkanin ‘yan Nijeriya da abin ya shafa da su kiyaye matakan tsaro da kuma tuntuɓar ofishin jakadanci mafi kusa domin yin rijista da samun ƙarin umarni.”
Baya ga haka, Gwamnatin Tarayya ta sake kira da a dakatar da faɗa tsakanin Isra’ila da Iran, tare da buƙatar ɓangarorin su rungumi tattaunawa, su mutunta dokokin kare haƙƙin ɗan Adam na duniya, kuma su bai wa rayuwar fararen hula muhimmanci.
Ma’aikatar ta jaddada cewa Nijeriya na goyon bayan hanyoyin warware rikici ta hanyar lumana da kuma tallafa wa zaman lafiya a yankuna da duniya baki ɗaya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp