Matatar mai ta Dangote ta sanar da fara dakon man fetur da dizal a fadin kasar daga ranar 15 ga Agusta, 2025. A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, matatar ta bayyana cewa shirin zai hada da ‘yan kasuwa, masu gidajen mai, masana’antun, kamfanonin sadarwa, kamfanonin jiragen sama, da sauran manyan masu amfani da man a fadin kasar nan.

A wani bangare na dabarun kasuwanci, matatar Dangote za ta yi dakon man kyauta, domin kawar da tsadar sufuri da kuma inganta harkar kasuwancin matatar a duk fadin kasar. Domin saukaka aikin, matatar ta sayo sabbin tankunan dakon man mai amfani da iskar Gas (CNG) 4,000, wadanda za su zama kashin bayan dakon kayan zuwa inda ake bukata.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Binciken CGTN: Za A Ci Gaba Da Nuna Kyakkyawan Fata Ga Bunkasar Sin Nan Da Shekaru 5

Bayanin da ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS ya yi a baya-bayan nan game da hasashe kan tattalin arzikin kasar Sin cikin shekaru biyar masu zuwa ya jawo hankalin duniya sosai. Kuma sakamkon binciken jin ra’ayoyin jama’a da CGTN na babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na Sin wato CMG ya yi a tsakanin masu bayyana ra’ayoyi 47,000 a kasashe 46 daga shekarar 2023 zuwa 2025, ya nuna jama’ar sun nuna yakini game da karfi da juriyar tattalin arzikin kasar Sin.

Binciken ya nuna cewa, yawancin masu bayyana ra’ayoyin daga sassan duniya suna da kyakkyawan fata ga tattalin arzikin kasar Sin wajen samun bunkasa mai kyau a dogon lokaci, inda amincewarsu ta kai kashi 74.7 bisa dari, da 81.3 bisa dari, da kuma 81.9 bisa dari cikin shekaru uku a jere.

Binciken da aka yi a bana ya kuma nuna cewa, masu bayyana ra’ayoyin suna da kwarin gwiwa game da samun damammaki masu kyau a kasuwar Sin a cikin yanayin kasa da kasa mai sarkakiya da tashe-tashen hankula. A cikinsu akwai kashi 79.8 bisa dari da suka bayyana cewa, babbar kasuwar Sin ta ba da muhimman damammaki ga kasashen da suke gudanar da kasuwanci a ciki.(Safiyah Ma)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Za a fara yi wa ɗaliban jami’o’i gwajin ƙwaya — Gwamnatin Nijeriya
  • Yadda Yajin Aikin Ma’aikatan Jinya Ya Bar Baya Da Kura A Asibitocin Jihar Filato
  • NNPCL ya sake haƙa sabbin rijiyoyin man fetur 4 a Kolmani
  • Kamfanin NNPCL ya sake haka sabbin rijiyoyin man fetur 4 a Kolmani
  • Hukumar Kula da Da’ar Ma’aikata Za Ta Fara Daukar Bayanai Ta Yanar Gizo
  • Binciken CGTN: Za A Ci Gaba Da Nuna Kyakkyawan Fata Ga Bunkasar Sin Nan Da Shekaru 5
  • Matatar Mai Ta Fatakwal Ba Ta Siyarwa Ba Ce – NNPC
  • Fiye Da Kamfanoni 30,000 Masu Zuba Jari Daga Waje Aka Kafa A Sin A Rabin Farkon Bana
  • Gwamnatin Katsina Ta Fara Bayar Da Maganin Zazzabi Kyauta A Asibitoci
  • NiMet Ta Yi Hasashen Samun Mamakon Ruwan Sama A Sassan Nijeriya Cikin Kwana 3