Dalilin Mara Wa Tinubu Baya Ba Tare da Ambaton Shettima Ba – Shugaban APC Na Arewa Maso Gabas
Published: 17th, June 2025 GMT
“Na ce Shettima ɗanmu ne, kuma muna alfahari da shi. Na kuma gode wa Tinubu bisa yadda ya bai wa ‘yan Arewa maso Gabas muƙamai masu gwaɓi kafin na nemi a mara masa baya,” in ji Salihu.
A lokacin taron, wasu matasa sun kusan kai masa hari, amma ya ce hakan ya faru ne saboda wasu ba su fahimci abin da ya yi ba.
Ya kuma jaddada cewa a tsarin jam’iyya, mutum ɗaya ne kawai ake zaɓa a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa a lokacin zaɓen fidda gwani, kuma shi ne ke da ‘yancin zaɓar mataimakinsa.
“Ba a daidaita tikitin shugaba da mataimaki a zaɓen fidda gwani. Ɗan takara kawai ake zaɓa, kuma yana da ‘yancin zaɓar wanda zai mara masa baya,” in ji shi.
Salihu ya kuma ƙaryata jita-jitar cewa akwai saɓani tsakanin Tinubu da Shettima.
Ya zargi wasu da ya kira “’yan kasuwar rikici” da ƙoƙarin ɓata lamarin domin amfanin kansu.
“Waɗanda ke yaɗa irin waɗannan labarai suna neman cin moriyar rikicin ne. Ba a gudanar da harkokin jam’iyya a dandalin sada zumunta ko a jaridu ba, a ofishin jam’iyya ake yin hakan,” in ji shi.
A ƙarshe, Salihu ya roƙi mambobin jam’iyyar da al’umma su guji yarda da jita-jita, yana mai cewa jam’iyyar APC na nan daram, babu wata matsala.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Arewa Maso Gabas
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu Ya Taya Amusan Da Gumel Murnar Samun Nasarori A Ɓangarori Daban-daban
Shugaban ya yaba da abinda ya kira kwarewa da juriya irin na Amusan, tare da cewa aikinta ya sake misalta irin daukakar da yan Nijeriya za su iya samu ta hanyar aiki tukuru da nuna kwazo, Tinubu ya yi fatan Gumel da Amusan su ci gaba da samun nasara a ayyukansu tare da ba su tabbacin gwamnati za ta ba su cikakken goyon baya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp