Wang Yi Ya Yi Tsokaci Kan Sakamakon Ziyarar Shugaba Xi A Kazakhstan
Published: 18th, June 2025 GMT
An gayyaci shugaban kasar Sin Xi Jinping zuwa kasar Kazakhstan, daga ranar 16 zuwa 18 ga watan Yunin shekarar 2025, don halartar taron koli karo na biyu na Sin da tsakiyar Asiya. A karshen ziyarar, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi wa manema labarai karin haske game da lamarin.
Wang Yi ya ce, babban abin da ya fi daukar hankali a wannan taro shi ne sanarwar da shugaba Xi Jinping ya yi ta “Ruhin Sin da Tsakiyar Asiya”.
Bugu da kari, dangane da halin da ake ciki a yankin Gabas ta Tsakiya, shugaba Xi Jinping ya yi nuni da cewa, kasar Sin na adawa da duk wani abu da zai kawo cikas ga ‘yancin kai, tsaro da martabar yankunan sauran kasashen duniya. Kuma shugabannin kasashen yankin tsakiyar Asiya sun yi kyakkyawan nazari kan rawar da kasar Sin take takawa a harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya.
Wang Yi ya kara da cewa, abu mafi muhimmanci game da wannan taro shi ne, shugabannin kasashen shida sun rattaba hannu tare a kan “Yarjejeniya ta dindindin game da kyakkyawar makwabtaka, da sada zumunci da kuma hadin gwiwa”, wadda ta tsara ka’idar sada zumunci bisa doka, inda hakan ya zama wani sabon ci gaba da aka samu a tarihin dangantakar da ke tsakanin kasashen shida. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: tsakiyar Asiya
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Ta Daga Zuwa Mataki Na 10 A Jadawalin GII Na Kasashen Dake Kan Gaba A Fannin Kirkire-Kirkire
Cikin jadawalin GII na 2025, kasashe masu karanci da matsakaicin kudin shiga 17, sun taka rawar gani fiye da yadda aka yi hasashe, bisa matsayin ci gabansu, yayin da kasashen Afirka dake kudu da hamadar Sahara ke kan gaba, cikin kasashe mafiya samun ci gaban kirkire-kirkire, inda kasashen Afirka ta Kudu, da Senegal da Rwanda ke kan gaba a jerin kasashen shiyyar. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp