Aminiya:
2025-09-18@00:41:39 GMT

Mun shirya yin sulhu da ’yan bindiga — Gwamnatin Sakkwato

Published: 18th, June 2025 GMT

Gwamnatin Jihar Sakkwato, ta bayyana cewa ta shirya zama da ’yan bindiga domin tattaunawa idan har suna da niyyar ajiye makamansu su rungumi zaman lafiya.

Wannan bayani ya fito ne daga Hadimi na Musamman kan Harkokin Tsaro na Gwamna Ahmed Aliyu, Kanal Ahmed Usman (mai ritaya).

Sojoji sun raunata shugaban ISWAP na Najeriya, Albarnawi Litar fetur za ta iya komawa N1,000 a Najeriya saboda yakin Isra’ila-Iran – Masana

Hadimin ya ce gwamnatin jihar na son tattaunawa don samar da zaman lafiya fiye da ci gaba da tafka yaƙi.

Gwamnatin ta ce a tarihi, an fi samu damar warware rikice-rikice da dama ta hanyar yin sulhu, ba ta hanyar amfani da ƙarfi kaɗai ba.

Saboda haka, jihar za ta iya tattaunawa da duk ’yan bindigar da suka yi niyyar miƙa wuya su dawo cikin al’umma lafiya.

Haka kuma, gwamnatin jihar ta nuna godiya ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, shugabannin rundunonin tsaro, da dukkanin jami’an tsaro da ke aiki wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

“Muna godiya matuƙa da sadaukarwarsu. Allah Ya jikan jarumanmu da suka rasu, ya bai wa iyalansu haƙuri,” in ji sanarwar.

Gwamnatin ta yaba da shirin da Gwamnatin Tarayya ke yi na tura masu gadi daji domin inganta tsaro.

Amma ta jaddada cewa dole ne a tabbatar da sahihanci da amincewar al’umma wajen ɗaukar aikin.

Ta kuma ce dole ne a sanya masu gadin daji su yi aiki ne ƙarƙashin kulawar hukumomin tsaro domin hana aikata ba daidai ba.

Sanarwar ta ƙara da cewa dole ne a tabbatar da kyakkyawar sadarwa tsakanin masu gadin daji da al’umma.

Ta ce wannan zai taimaka wajen samar da amana da goyon baya daga mutanen da ake son karewa.

Hakazalika, Gwamnatin ta jaddada cewa tana da cikakken ƙudiri wajen samar da zaman lafiya da tsaro ga kowa.

Ta ce ba za ta tsaya ko ta yi ƙasa a guiwa ba wajen tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a faɗin jihar.

Wannan mataki yana nuna cewa gwamnat8i na son yin haɗin gwiwa da al’umma domin samar da dawwamammen zaman lafiya.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Bindiga gwamnati matsalar tsaro Sakkwato tattaunawa zaman lafiya Gwamnatin ta

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Sudan Ta Ce: Babu Sulhu Da ‘Yan Tawayen Kasar Na Kungiyar Rapid Support Forces

Gwamnatin Sudan ta ce: Babu batun sasantawa da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces na kasar wadanda take daukansu a matsayin ‘yan tawaye

Gwamnatin Sudan ta yi watsi da shawarar sasantawa da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces (RSF) da kasashen kasashe masu shiga Tsakani suka gabatar, tana mai jaddada cewa, tana mutunta duk wani kokari da zai taimaka wajen kawo karshen yakin kasar, matukar dai ya mutunta diyaucin kasar da halaltattun hukumomin kasar.

Sa’o’i kadan bayan kaddamar da shirin na bangarori hudu masu shiga tsakani wanda ya hada da Masar, Amurka, Saudiyya, da Hadaddiyar Daular Larabawa, na kiran zaman lafiya a Sudan da kawo karshen yakin, dakarun kai daukin gaggawa sun kai hari kan tashar samar da wutar lantarki da ma’ajiyar man fetur da kuma filin jirgin saman Kenana na jihar White Nile da jiragen sama marasa matuka ciki.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi kira da a ba da sanarwar yin watsi da shirin, inda ta yi nuni da cewa, yaƙin na da nasaba da al’ummar Sudan, kuma za ta tunkare shi, ta kuma yanke shawara da kansa.

Wani mai sharhi kan al’amuran siyasa Youssef Abdel Manan ya shaidawa tashar talabijin ta Al-Alam cewa: “Kasashen hudu masu siga tsakani ba su da wani hakki, ko na hukuma, ko na dabi’a, ko na siyasa, ko na kasa da kasa, da zai sanya su zama masu kula da al’ummar Sudan.”

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Kasashen Larabawa da na Musulmi na taron gaggawa kan harin Isra’ila a Qatar September 15, 2025 Hamas ta bukaci kasashen musulmi da na Larabawa su dauki mataki mai tsari kan Isra’ila September 15, 2025 Rabin Sojojin Isra’ila da suka ji rauni a yakin Gaza na fama da ciwon damuwa September 15, 2025 Sudan ta soki takunkuman da Amurka ta kakaba mata September 15, 2025 Dakarun Sojin Yamen Sun Kai Hari Kan Filin Jirgin Saman Ramon Na Isra’ila. September 14, 2025 Isra’ila Za ta Gamu Da Mummunar Martani Idan Tayi Gigin Afkawa Iran September 14, 2025 Ministocin Harkokin Wajen Kasashen Larabawa Da Na Musulmi Sun Fara Taro A Qatar. September 14, 2025 Gwamnatin Najeriya Ta Sanar Da Sabon Sharadi Na Bude Asusun Banki September 14, 2025 An Zabi Issa Tchiroma A Matsayin Dan Takara Daya Tilo A Kamaru September 14, 2025 Kasar Iran Ta Yi Fatali Da Zarge-Zargen Da Kungiyar G7 Da Kawayenta Suka Yi Kanta September 14, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Sabon Tsarin Kula Da Lafiyar Mata Masu Juna Biyu Da Kananan Yara
  • Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci da ya sanya a Ribas
  • Gwamnatin Kano Ta Inganta Cibiyoyin Horas Da Sana’o’i Domin Dakile Aikata Laifuka Tsakanin Matasa
  • Pezeshkian: Saudiyya Na Iya Taka Muhimmiyar Rawa Wajen Samar Da Hadin Kan Kasashen Musulmi
  • Baqa’i: Kowace Kasa A Duniya Tana Da Hakkin Mallakar Makamashin Nukiliya Na Zaman Lafiya
  • ’Yan bindiga sun kai wa sojoji hari a ranar da ake zaman sulhu
  • Ɗan Majalisar Tarayya Ya Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-haren Ta’addanci A Sakkwato 
  • Gwamnatin Neja Ta Musanta Rahoton Hana Da’awa A Jihar
  • Sulhu Da ‘Yan Bindiga Ya Fara Shan Ƙasa, Sun Yi Garkuwa Da Masallata A Zamfara 
  • Gwamnatin Sudan Ta Ce: Babu Sulhu Da ‘Yan Tawayen Kasar Na Kungiyar Rapid Support Forces