Yaƙin Iran da Isra’ila: Amurka za ta tura jami’anta don tattaunawa da Tehran
Published: 17th, June 2025 GMT
Shugaban Ƙasar Amurka, Donald Trump ya ce yana neman ganin an kawo karshen rikicin nukiliyar ƙasar Iran gaba ɗaya, a yayin da aka shiga kwana na biyar a yaƙin da ya ɓarke tsakanin Iran da Isra’ila.
Trump ya bayyana shirinsa na tura manyan jami’an ƙasarsa zuwa birnin Tehran domin tattaunawa da hukumomin Iran a game da lamarin.
Ya bayyana haka ne a yayin da yake hawa jirgi domin barin ƙasar Kanada, inda ya halarci taron ƙasashen G7.
A yayin taron, shugabannin ƙasahen sun bayyana Iran a matsayin barazana, da bai kamata a bari ta mallaki makaman nukiliya ba. A ɗaya bangaren kuma sun bayyana ’yancin Isra’ila na kare kanta.
Matatar man Isra’ila ta daina aiki bayan harin Iran Sarki ya yi barazanar hana yin Musulunci a garinsa bayan dodanni sun kai wa Musulmi hari NAJERIYA A YAU: Yadda Cin Ganyayyaki Ke Yi Wa ‘Yan Najeriya WahalaTrump wanda ya bar taron tun kafin a kammala ya bayyana cewa abin da ke gabansa na wuce batun tsagaita wuta da Amurka ke nema tsakanin Iran da Isra’ila.
Ya bayyana cewa ƙasashen biyu da a halin yanzu suke ci gaba da yi wa juna luguden bama-bamai ba su sassauta ba, amma ya sha nanata cewa akwai yiwuwar kawo ƙarshen rikicin da wuri, idan Iran ta amince da tayin da Amurka ta yi mata.
Makon jiya ne jiragen Isra’ila suka ƙaddamar da hare-haren ba-zata a Iran inda suka kashe wasu manyan kwamandoji da masana kimiyyar nukiliya.
Isra’ila ta yi iƙirarin karɓe ikon sararin samaniyar Iran, kuma za ta tsananta kai hare-hare a nan gaba.
Hare-haren sun halaka mutane da dama a sassan kasashen biyu.
Rahotanni a cikin dare sun nuna yadda na’urorin tsaron sararin samaniyar Iran ke kakkaɓo makamai a sassan ƙasar.
Rundunar juyin juya halin Musulunci na Iran ta bayyana cewa za ta sake harba tarin rokoki zuwa Isra’ila.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Iran Isra ila makaman nukiliya
এছাড়াও পড়ুন:
Ɗangote zai gina ɗakunan kwanan ɗalibai 250 a Jami’ar Ilorin
Babban attajirin Afirka kuma Shugaban Rukunin Kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Ɗangote, ya ɗauki nauyin gina ɗakunan kwanan ɗalibai masu gadaje 250 da Babban Masallacin Juma’a na Ilorin ya tsara a Jami’ar Ilorin da ke Jihar Kwara.
An kiyasta aikin zai ci kusan naira biliyan 1.1, kuma an ƙaddamar da shi ne domin samar da hanyar samun kuɗin kula da masallacin.
Ana sa ran kuɗaɗen haya da za a samu daga ɗaliban da za su zauna a wurin zai rika shiga asusun kula da masallacin.
Sakataren kwamitin amintattu na masallacin, Alhaji Shehu AbdulGafar, ya shaida wa manema labarai a Ilorin cewa Ɗangote ya riga ya sanar da su cewa zai ɗauki nauyin aikin gaba ɗaya.
Cire tallafin man fetur shi ne abin da ya dace —Sarki Sanusi II NAJERIYA A YAU: Yadda Wasu Al’ummomi Suke Kare Kansu Daga Barnar Ambaliyar RuwaYa ce an riga an rattaba hannu kan yarjejeniya da Jami’ar Ilorin wadda ta ba wa masallacin damar mallaka da gudanar da ɗakin kwanan ɗaliban na tsawon shekaru 21 kafin a miƙa shi ga jami’ar.
Baya ga aikin ginin, Ɗangote ya kuma yi alƙawarin bayar da tallafin Naira miliyan 5 a kowane wata domin kula da masallacin har sai an kammala aikin.
AbdulGafar ya ce wannan taimako zai rage nauyin kuɗin aikin, tare da tabbatar da ɗorewar ayyukan masallacin.
Ya ƙara da cewa ɗakin kwanan zai taimaka wajen rage matsalar ƙarancin wurin kwana ga ɗaliban jami’ar.
Shugabannin al’umma da sauran masu ruwa da tsaki sun yaba wa Ɗangote, sun bayyana wannan mataki a matsayin abin koyi na yadda za a iya haɗa kai tsakanin cibiyoyin addini da ’yan kasuwa wajen ci-gaban al’umma.