Aminiya:
2025-07-31@19:33:59 GMT

Sabon harin Iran ya hallaka mana mutum 8 – Isra’ila

Published: 16th, June 2025 GMT

Isra’ila ta ce mutum takwas sun mutu a daren ranar Litinin sakamakon sabon harin da Iran ta kai a biranen Tel Aviv da Haifa da wasu sassa na ƙasar.

Wannan na zuwa ne a matsayin ci gaba daga jerin hare-hare da Iran ke kai wa tun bayan da Isra’ila ta fara kai mata hari makonnin da suka wuce.

NAJERIYA A YAU: Dalilan Durƙushewar Sababbin Sana’o’i Tun Ba A Je Ko’ina Ba Iran ta kai sabbin hare-hare birnin Tel Aviv da Haifa

Yanzu haka, adadin mutanen da hare-haren Iran suka kashe a Isra’ila ya kai 24, yayin da mutane sa.

a da 300 ke kwance a asibitoci saboda raunuka.

Isra’ila ta ce a martaninta, jiragen yaƙin ƙasar sun kai hari a birnin Tehran, babban birnin Iran, inda suka lalata wata hedikwatar dakarun juyin juya hali.

Haka kuma sun kai farmaki a wasu cibiyoyi da Iran ke adana makamai a tsakiyar ƙasar.

An fara wannan rikici ne bayan da Isra’ila ta kai hari da asubahin ranar Juma’a a Iran.

Iran ta ce a wannan harin, mutane sama da 200 ne suka mutu.

Wannan hari ya fusata gwamnatin Iran, inda ta fara mayar da martani da hare-hare a Isra’ila.

A baya ma, ana zargin Isra’ila da kai hare-hare da dama a Iran, musamman kan dakarun da ta ke zargi da taimaka wa ƙungiyoyin da ke barazana gare ta, kamar Hezbollah da Hamas.

Rikicin ya ci gaba da tsananta, yayin da kowane ɓangare ke kai farmaki ga ɗaya, al’ummar ƙasashen biyu na ci gaba da jikkata da mutuwa.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Iran Isra ila yaƙi Isra ila ta

এছাড়াও পড়ুন:

An Fara Sabon Zagayen Tattaunawar Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka A Sweden

Tawagogin wakilan kasashen Sin da Amurka sun hallara a kasar Sweden yau Litinin, domin fara wani sabon zagayen tattaunawa game da cinikayya da tattalin arziki. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Hare-hare: ’Yan bindiga sun raba mutum 5,000 da muhallansu a Katsina
  • Tawagar Iran Ta Fice A Taron Majalisun Dokokin Kasashen Duniya A Lokacin Jawabin Wakilin Isra’ila
  • Sojojin Yemen Sun Kai Zafafan Hare-Hare Kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila Guda Uku  
  • Remi Tinubu ta bai wa waɗanda harin Benuwe ya shafa tallafin Naira biliyan ɗaya
  • Remi Tinubu ta ba da tallafin Naira biliyan ɗaya ga waɗanda harin Benuwe ya shafa
  • ’Yan bindiga sun kashe mutum 5 a sabon hari a Alkaleri
  • Araqchi: Iran Zata Mayar Da Martanin Da Ba Zai Yiwu A Boye Ba  Kan Duk Wani Harin Wuce Gona Da Iri Kanta
  • Kasar Faransa Ta Yi Allah Wadai Da Harin Ta’addancin Da Aka Kai Birnin Zahedan Na Kasar Iran
  • An fara shigar da kayan agaji a Gaza
  • An Fara Sabon Zagayen Tattaunawar Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka A Sweden