Majalisa ta aike wa Tinubu kudurorin dokar haraji domin ya rattaba musu hannu
Published: 18th, June 2025 GMT
Majalisar Dokoki ta kasa ta ce ta aike wa Shugaban Kasa Bola Tinubu kudurorin dokar harajin da ta amince da su a hukumance domin ya rattaba musu hannu su zama doka.
Shugaban Kwamitin Yada Labarai na Majalisar Dattawa, Sanata Yemi Adaramodu (APC, Ekiti) ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai ranar Talata a Abuja.
A bara ne dai Tinubu ya aike wa majalisar kudurorin domin su yi nazarinsu sannan su amince da su a matsayin doka.
Ambaliyar Mokwa: Har yanzu muna neman mutum 700 – Gwamnatin Neja DAGA LARABA: Ko Kare Kai Daga Harin ‘Yan Ta’adda Zai Kawo Karshen Matsalar Tsaro?Kudurorin dai a baya sun yamutsa hazo sosai a zaurukan majalisun da ma a fadin kasa, kafin daga bisani majalisun na wakilai da dattawa su amince da su.
Sanata Yemi ya ce, “Eh, yanzu kudurin ya bar hannunmu, yana kan hanyarsa ta zuwa wajen Shugaban Kasa domin ya sanya masa hannu ya zama doka.
“Kudurorin haraji irin wadannan suna bukatar taja da tsifa sosai. Dole bangarorin masana shari’a na zaurukan majalisun biyu su tabbatar kudurorin sun yi daidai da dokokin da ake da su a kasa kafin su tura wa Shugaban Kasa.
“Ba aiki ba ne na kwana biyu ko uku. Bayan an kammala aikin daidaita su kuma Akwun Majalisar Dokoki ta Kasa zai mayar da su kundi daya. Bayan haka ne kawai Shugaban Majalisar Dattawa da ta Wakilai za su sa hannu a aike da su,” in ji Sanatan.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Kudurin dokar haraji
এছাড়াও পড়ুন:
Za a kashe biliyan 712.26 don yi wa filin jirgin saman Legas garanbawul
Majalisar Zartarwa ta Kasa ta amince da kashe Naira biliyan 712.26 don yi wa wani sashe na filin jirgin saman a Murtala Muhammad da ke Legas garambawul.
Hakan dai ya biyo bayan zaman majalisar wanda Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya jagoranta a Abuja ranar Laraba.
NAJERIYA A YAU: Me dokar kasa ta ce kan karin wa’adin aiki da Shugaban Kasa ke yi? Za a fara yi wa ɗaliban jami’o’i gwajin ƙwaya — Gwamnatin NijeriyaAikin dai wani bangare ne na Naira biliyan 900 da aka ware domin inganta harkokin sufurin jiragen sama a fadin Najeriya.
Ministan Harkokin Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo ne ya bayyana hakan jim kadan da kammala taron majalisar, inda ya ce tuni har an ba da kwangilar aikin ga kamfanin gine-gine na kasar China (CCECC).
A cewar Ministan, aikin ya kuma kunshi canza kayayyakin da ake amfani da su a wurin saukar jirage na filin daga na da zuwa na zamani.
Keyamo ya kuma ce majalisar ta kuma amince a kashe Naira biliyan 49.9 wajen aikin katange filin jirgin na Legas domin a inganta tsaro a cikin shi,
Katangar mai tsawon kilomita 14.6 wacce ta karfe ce, za kuma a saka mata na’urori a jikinta da kyamarorin CCTV da fitilu masu amfani da hasken rana da kuma tituna a gefenta.
“Duk wanda ko kuma duk abin da ya rabi katangar za mu gan shi cikin gaggawa sannan a nuna wajen da yake,” in ji Minista Keyamo.