Sojojin Nijeriya sun kashe gomman ’yan ta’adda a Tafkin Chadi
Published: 18th, June 2025 GMT
Rundunar sojin Nijeriya ta sanar dakashe gomman ’yan ta’adda na ISWAP da Boko Haram da suka yi ƙoƙarin kutsawa cikin sansanin sojin ruwan ƙasar a yankin Tafkin Chadi.
Hakan dai na kunshe cikin wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na X ranar Laraba wadda ta ce ‘yan ta’addan sun yi ƙoƙarin kutsawa cikin sansanin sojojin ne da misalin ƙarfe 2 na dare, inda suka yi ƙoƙarin lalata sabbin motocin tafiya a fadama waɗanda gwamnatin Jihar Borno ta saya domin yashe hanyoyin ruwa.
Sai dai jami’ai a sansanin sojin ruwan Nijeriya da ke Tafkin Chadin sun jajirce wajen hana su kutsawa, inda aka yi ta musayar wuta har tsawon sama da sa’o’i biyu kafin aka kai musu ɗauki daga Baga, lamarin da ya tilasta wa ‘yan ta’addan ja da baya ba tare da sun kai ga motocin tafiya cikin fadamar ba, in ji sanarwar.
Baya ga kashe gomman ‘yan ta’addan, sanarwar ta ce sojojin sun yi nasarar kwato ababe masu fashewa yayin da wasu daga cikin jam’ian tsaron suka ji rauni.
“Ɓangaren sojin sama [na rundunar] na bin sawun [‘yan ta’addan] a kan ruwa domin ƙara kassara su,” in ji sanarwar.
A makonnin baya bayan nan dai hare-haren ’yan Boko Haram suna ƙoƙarin dawowa arewa maso gabashin Nijeriya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yan ta addan
এছাড়াও পড়ুন:
Trump Ya Ayyana Nijeriya A Matsayin Ƙasar Da Rayuwar Kiristoci Ke Cikin Hatsari
“Amurka ba za ta tsaya kawai tana kallo ba yayin da irin waɗannan ta’addancin ke faruwa a Nijeriya da sauran ƙasashe.
“Mun shirya, muna da ƙarfi da niyyar kare Kiristoci a faɗin duniya,” in ji Trump.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA