Kungiyar cinikayya ta duniya wato WTO, ta kira taro karo na 63 mai taken “Ba da tallafin ciniki” a jiya Talata a birnin Geneva. Yayin da aka tattauna bisa ajandar “Makomar hadin gwiwar kasashe masu tasowa da saurin bunkasuwa”, Sin ta yi cikakken bayani kan dabaru, da fasahohi da Sin take da su a fannin tallafawa sauran kasashe masu tasowa wajen gina manyan ababen more rayuwa, da gaggauta karfin samar da tsare-tsaren cinikayya, matakin da ya samu karbuwa matuka daga mahalarta taron.

A bangaren nahiyar Afirka, kasar Mozamqiue ta darajanta kokarin da Sin take yi na karawa kasashe masu tasowa kwarin gwiwar gina ingantattun manyan ababen more rayuwa, da gaggauta karfin samar da tsare-tsare, karkashin tsarin hadin gwiwar kasashe masu tasowa, matakin ya bayyana niyyar Sin na cika alkawuran da take yi na tabbatar da tsarin gudanar da cinikayya tsakanin mabambantan bangarori, da amfanar da al’ummun kasashensu. A bangaren wakilcin kasashe mafiya karancin ci gaba, wakilin Nepal ya bayyana godiya ga taimakon da Sin take ba su, a bangaren zamanantar da na’urorin kwastam, da kafa dokar ciniki, da samun ci gaba mai dogaro da yanar gizo da sauransu.

Ban da wannan kuma, tawagar Kamaru ta yi godiya ga gudunmawar da Sin take bayarwa ga nahiyar Afirka a bangaren gina manyan ababen more rayuwa, da tabbatar da zaman doka da oda da habaka karfinsu, matakan da suka ingiza bunkasar nahiyar a dukkanin fannoni masu dorewa. A nata bangare, tawagar kasar Tanzaniya, ta jinjinawa tallafin da Sin take baiwa kasashen Afirka a bangaren ciniki, tana godiya da kokarin da Sin take yi na zurfafa hadin gwiwar kasashe masu tasowa, bisa hanyar kirkire-kikire da take bullowa da su, ta yadda kasashe masu tasowa za su shiga a dama da su cikin tsarin cinikin duniya yadda ya kamata. (Amina Xu)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: kasashe masu tasowa

এছাড়াও পড়ুন:

Ranar Foliyo Ta Duniya: Muna Fatan Ganin Karshen Cutar Foliyo A Jihar Katsina -Zulaihat Dikko Radda

A cewar ta a cikin shekarar 2024 jihar Katsina kawai ta samu masu wannan cuta mutum 17 tare da guda biyu a karamar hukumar Danmusa a cikin wannan shekara

Haka kuma Hajiya Zulaihat Radda ya bada tabbacin cewa kowane yaro an tabbatar da ya amshi allurar Riga-kafin shan Inna

Ana jawabin wakilin asusun tallafawa yara na UNICEF na ofishin Kano, Rahama Mohammed Farah ta yabawa kokarin jihar Katsina na dawo da sabon yunkurin kawar cutar shan Inna a Nijeriya baki daya

Ya kuma bayyana cewa asusun kula da kananan yara na UNICEF Yana hadin gwiwa da gwamnatoci da hukumomi da masu ruwa da tsaki a kananan hukumomi domin ganin wajen fadakar da al’umma akan allurar Riga-kafin shan Inna a jihar Katsina.

Shima da yake jawabi shugaban hukumar lafiya a matakin farko ta Jihar Katsina Dakta Shansudeen Yahaya ya yi alkawarin cigaba da wayar da kan al’umma akan wannan cuta ta shan Inna da sauran cututtuka masu kashe yara a kananan hukumomi 34 na jihar Katsina

Wadanda suka shaida wannan bikin ranar ‘Polio’ ta duniya sun hada da hukumar lafiya ta WHO da kuma masu lalurar cutar shan Inna da wakilan asusun UNICEF da matan shugabannin kananan hukumomi 34 na jihar Katsina

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Yan Nijeriya Na Ɗanɗana Kuɗarsu Kan Jinkirta Cire Tallafin Mai – Sarki Sanusi October 31, 2025 Manyan Labarai Allah Ya Kai Manzon Allah (SAW) Muƙami Na Babban Yabo A Cikin Komai October 31, 2025 Manyan Labarai Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP October 31, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Babban Burina Zama Fitacciyar Jaruma A Duniya —Aisha Umar
  • ‘An Kashe Masu Zanga-zanga Akalla 500 a Tanzania’
  • Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa
  • Gwamnatin Yobe ta ƙaddamar da shirin amfani da ma’adanai
  • Makarantar Kogi Poly Ta Bankaɗo Masu Ƙirƙirar Takardun Kammala Karatu na Bogi
  • Manoma a Jigawa Sun Jinjinwa Kungiyar Sasakawa Africa Bisa Bada Tallafi a Harkar Noma
  • Ranar Foliyo Ta Duniya: Muna Fatan Ganin Karshen Cutar Foliyo A Jihar Katsina -Zulaihat Dikko Radda
  • NAJERIYA A YAU: Dalilan Da Daliban Makarantar Kudi Suka Fi Na Gwamnati Kokari
  • Sin Ta Fitar Da Jerin Sakamakon Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Tawagar Kasar Da Ta Amurka Suka Cimma 
  • Xi Jinping: Sin Da Amurka Za Su Iya Hada Kai Don Sauke Nauyin Dake Wuyansu Na Manyan Kasashe Da Daukar Ainihin Matakai