Aminiya:
2025-12-11@16:03:26 GMT

Isra’ila ta ƙaddamar da sabon hari a Zirin Gaza

Published: 18th, March 2025 GMT

Isra’ila ta keta yarjejeniyar tsagaita wuta inda ta ƙaddamar da sabbin hare-hare kan Falasɗinawa a Zirin Gaza.

Sabbin hare-haren da Isra’ila ta ƙaddamar sun kashe fiye da mutum 200 ciki har da mata da yara tare da jikkata daruruwa a yayin da ake ci gaba da kai gawawwaki asibiti.

Mahaifina ne kaɗai shugaban da bai damu ya azurta kansa ba — Seyi Tinubu Abba ya rantsar da sabon Kwamishinan Gidaje na Kano

Hamas ta ce Isra’ila ta kai harin na ba-zata ne kan fararen hula da ta shammata a ƙoƙarin ta na keta yarjejeniyar tsagaita wutar da suka ƙulla tun a ranar 19 ga watan Janairu.

Kazalika, dakarun tsaron Isra’ila (IDF) sun ce sun kai hari kan abin da suka kira wuri mai ‘barazanar ta’addanci’ na Hamas.

Wannan dai shi ne hari mafi girma da aka kai a Gaza tun bayan da aka fara tsagaita wuta a ranar 19 ga watan Janairu yayin da aka gaza cimma matsaya a tattaunawar tsawaita wa’adin tsagaita wutar na Gaza..

Bayanai sun ce galibin waɗanda hare-haren suka rutsa da su mutane da ke cin abincinsu na Sahur kafin fitowar alfijir.

Majiyoyi sun ce sama da jiragen yaƙin Isra’ila 20 ne suka yi shawagi a sararin sama, sannan suka soma luguden wuta a garuruwan Gaza da Rafah da Khan Younis.

Firayim Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da Ministan Tsaro Isra’ila Katz ne suka ba da umarnin kai hare-haren a safiyar ranar Talata, kamar yadda wata sanarwa daga ofishin Firayim Minista ta sanar.

BBC ya ruwaito cewa an kashe Mahmoud Abu Wafah, mataimakin ministan harkokin cikin gida a Gaza kuma babban jami’in tsaron Hamas a yankin.

Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta ce kawo yanzu aƙalla Falasɗinawa 48,572 ne aka tabbatar da mutuwarsu yayin da wasu 112,032 suka jikkata a yakin da Isra’ila ke yi a Gaza.

Ofishin yada labarai na gwamnatin Gaza ya sabunta alƙaluman waɗanda suka mutu zuwa fiye da 61,700, yana mai cewa dubban Falasɗinawa da suka bace a ƙarƙashin baraguzan ginin ana kyautata zaton sun mutu.

Aƙalla mutane 1,139 ne aka kashe a Isra’ila a harin da Hamas ta jagoranta a ranar 7 ga Oktoba, 2023, sannan sama da 200 aka kama.

 

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Isra ila Isra ila ta

এছাড়াও পড়ুন:

Najeriya za ta buga wasan sada zumunta da Masar kafin fara gasar AFCON ta 2025

Tawagar Super Eagles ta Najeriya za ta buga wasan sada zumunta da ƙasar Masar kafin fara gasar Kofin Afrika da za a yi a Maroko.

Wasan zai gudana ne a ranar 11 ga wata. Disamba, da misalin ƙarfe 7 na dare, a filin wasa na Cairo da ke Masar.

EFCC ta tsare Malami kan binciken kuɗaɗen Abacha Real Madrid  za ta ɓarje gumi da Manchester City a Santiago

Za a yi wasan ne kwana shida kafin a fara gasar da ƙasashe 24 za su fafata a cikinta.

Najeriya za ta fara wasanta na farko a ranar 23 ga watan Disamba da Tanzania.

Ita kuwa Masar za ta buga wasanta na farko da Zimbabwe a ranar 22 ga watan Disamba.

A tarihi, Masar ce tafi lashe Kofin Afrika inda ta lashe gasar sau bakwai, yayin da Najeriya ta lashe sau uku.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Hamas : Isra’ila ta gaza cika alkawarin da ta dauka kan yarjejeniyar tsagaita wuta
  • Sakamkon Jin Ra’ayi: Yawancin Amurkawa suna adawa da yunkurin kai hari kan Venezuela
  • Iran Ta yi Tir Da Kisan Karen Dangin Isra’ila A Gaza A Ranar Yaki Da Kisan Kiyashi Ta MDD
  • Hamas Ta yi Tir Da Sabbin Matsugunan Yahudawa Da Isra’ila Ke yi A Yankunan Da Ta Mamaye
  • Najeriya za ta buga wasan sada zumunta da Masar kafin fara gasar AFCON ta 2025
  • Sakkwatawa na murnar kisan da sojoji suka yi wa mataimakin Bello Turji
  • RSF : Rabin ‘Yan jarida 67 da aka kashe a bana, a Zirin Gaza ne
  • Isra’ila ta sake kai hare-haren a kudancin Lebanon
  • MِِِِDD:  Kisan Kare Dangin Da Isra’ila Ta yi A Gaza Shi Ne Farko Da Yafi Jan Hankalin duniya
  • Sojoji sun kashe ’yan bindiga 13, sun ceto ’yan kasuwa a Sakkwato