Iran An Dauke Wa Mahdi Karubi Daurin Talalar Da Aka Yi Masa A Gida
Published: 18th, March 2025 GMT
Dan Mahadi Karubi, wanda yana ya jagoranci boren 2009 bayan zaben shugaban kasa, ya bayyana cewa an daukewa mahaifin nashi daurin talalar da aka yi masa bisa umarnin ma’aikatar sharia.
Shi dai Mahadi Karubi an yi masa daurin zaman gidan ne bayan hargitsin da ya jagoranta bayan zaben shugaban kasar da aka yi a 2009.
Husain Karubi ya fada wa kamfanin dillancin labarun “IRNA” cewa; An fada wa mahaifina cewa, Daga nan zuwa watan Aprilu zai iya gudanar da rayuwarsa ta yau da kullum ba tare da kaidi ba, amma daga yanzu zuwa lokacin zai iya sanar da jami’an tsaro inda yake son zuwa gabanin kwana daya.
Harigitsin day a biyo bayan zaben 2009 a Iran wanda ‘yan takara uku fitattu su ka tsaya, da su ne Ahmadinejad da ya lashe zaben, sai kuma Mirhusain Musawi da Mahdi Karubi. Wadanda ba su ci zaben ba, sun riya cewa an yi magudi a zaben, lamarin da mahukunta su ka kure shi saboda rashin wani dalili da madogara.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Tattauana Da Shugaban Hukumar IAEA
Shugaban hukumar makamshin Nujkliya ta MDD ya zanda da ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Aragchi kan al-amuran da suka shafi shirin nukliyar kasar Iran da kuma tattaunawar da ake gudana tsakanin ta da Amurka.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa a tattaunawa ta wayar tarho tsakanin jami’an guda biyu a jiya Lahadi, Grossi shugaban IAEA ya bayyana cewa ya ji dadin yadda JMI ta zabi tattaunawa da AMurka dangane da shirinta na makamashin Nukliya. Ya kuma bayyana cewa hukumarsa a shirye take ta gabatar da duk wani taimakon da JMI take bukata a yayin tattaunawar.
A nashi bangaren Abbas Araqchi ya bayyana cewa kasar Iran a shirye take ta bada hadin kai ga hukumar ta IAEA kamar yadda yarjeniyar NPT take bukata da kuma dokokin kasa da kasa.
Abbas ya fada masa inda aka kai ya zuwa yanzu a tattaunawa ba kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka, a biranen Mascat na kasar Omman da kuma Roma na kasar Italiya.
Ya zuwa yanzu dai kasashen biyu sun gudanar da taro har sau uku dangane da shirin Nukliyar kasar ta Iran, kuma bangarorin biyu sun bayyana amincewarsu da yadda tattaunawar take tafiya.