Aminiya:
2025-12-01@11:16:01 GMT

Tsofaffin furodusoshin Kannywood da aka daina jin ɗuriyarsu

Published: 18th, March 2025 GMT

Masana’antar Kannywood ta dade tana nishaɗantar da al’umma, musamman Hausawa da sauran kabilun Arewacin Najeriya.

A makon jiya Aminiya ta ruwaito a cewa kasuwancin fina-finan ya samu koma-baya matuƙa, wanda hakan ya sa wasu suke nuna yatsa ga furodusohin yanzu kan gaza shirya fim ɗin da za a iya haskawa a Netflix da sauran manyan hanyoyin nuna fina-finai da za su samar wa masana’antar kuɗin shiga.

NAJERIYA A YAU: Yadda Mai Karamin Karfi Zai Mallaki Muhalli Da Kudi Kalilan Isra’ila ta ƙaddamar da sabon hari a Zirin Gaza

Wannan ya sa Aminiya ta yi waiwayen wasu furodusohin da aka daina jin ɗuriyarsu a masana’antar.

Salisu Galadanchi – Shi ne Daraktan Fim din Turmin Danya, fim na farko a Kannywood, ya yi ritaya daga aikin gwamnati a Gidan Talabijin na CTV, yana zaune a Kano.

Umar Sheikh Mohammed: Shi ne mai Kamfanin Godiya and Dan Hassan wanda ya shirya fina-finan barkwanci, shi ma ya yi nukusani.

Bala Ahmed: Ana kiransa da Bala Sarauniya saboda rawar da ya taka wajen shiryawa da gabatar da finafinan Kamafanin Sarauniya Films a Kano.

Auwalu Mohammed Sabo shi ne Furodusan Kamfanin Sarauniya Films wanda suka yi finafinan gargajiya irin su Sangaya da Daskindaridi da Linzami da Wuta da sauransu. Yanzu yana aiki a Majalisar Dokokin Jihar Kano.

Ali Jindos Aneesa: Tsohon mai daukar hoto na masana’antar, wanda ya koma shirya fim. Shi ya kawo Saratu Daso Kannywood a inda ya sa ta a fim din sa Feleke.

Habibu Sani: Tsohon mai shirya finafinai na Kamfanin K Films Multi Services, kuma tsohon ma’aikacin Hukumar Tarihi da Al’adun Gargajiya ta Jihar Kano, shi ne Furodusan Saki Reshe 2 da Reshe Ya Juye da Mujiya 1 da na 2. Shi ne kuma ya jagoaranci Kungiyar AHFIP a zamanin Abubakar Rabo.

Auwalu Isma’il Marshal: Tsohon Shugaban Kungiyar Tumbin Giwa da ta koma Tumbin Giwa Films, ya jagoranci shirin finafinai, yanzu kuma Shugaban Kungiyar Dattawan Kannywood.

Adamu Mohammed. Shi ne mai Kamfanin Kwabo Films, wanda ya yi fim din Kwabon Masoyi daga littafinsa mai wannan suna da kuma Dan Almajiri na 1 da na 2.

Umar Bawa Dukku: Shi ne mai Kamfanin Dukku Productions wanda ya shirya finafinan barkwannci da dama. Shi ne kuma wanda ya fara buga fim a faifan SIDI da fim din sa mai suna Zainab a lokacin ana sakin finafinai a kaset.

Hamisu Lamido Iyan Tama: Shi ne mai Kamfanin Iyan Tama Multimedia, finafinan Gashin Kuma da Kilu Ta Ja Bau, na daga cikin finafinan da kamfaminsa ya shirya, baya ga buga wakoki na sauran finafinai da kuma fito da Ali Baba Yakasai wanda ya fara buga wa Rarara kida.

Abubakar A. S. Mai Kwai: Shi ne mai Kamfanin Mai Kwai Mobies, inda ya shirya kuma ya dauki nauyin finafinai irinsu Kona Gari, Munafikin Mata da sauransu.

Abdullahi Maikano: Mazaunin garin Kaduna ne, ya yi suna a shirya finafinai a baya, ya taba zama Shugaba Kungiyar MOPPAN

Yakubu Lere: Fitaccen furodusa da ya yi fim din Wasila na 1 da na 2 a karkashin kamfaninsa na Lerawa Films da kuma wasu finafinan. Ya taba zama mai ba Gwamnan Jihar Kaduna Shawara kan Harkar Yada Labarai.

Aminu Hudu: Mai Kamfanin ALMAH Productions, tsohon furodusa ne da ke garin Jos ya yi suna a harkar sayar da kaset kafin ya koma shirin fim a shekarun 1990.

Rabi’u HRB: Shi ne mai Kamfanin HRB Films mai ofishi a Kano daga baya ya koma Kaduna. Ya yi finafinai da yawa a ciki har Gyale da kuma Abin Sirri Ne.

 Ibrahim Dahiru: Shi ne mai Kamfanin 3SP a Jos, ya yi finafinai da dama a karkashin kulawar Abubakar da kuma Shehu.

Bala Anas Babinlata: Koda yake an fi saninsa a harkar rubutu da kuma bayar da umarni, amma ya yi finafinai na kansa a karkashin kamfaninsa Babinlata Films Sarma-Sarma na daya daga cikinsu.

Hajiya A’isha Halilu: Tana daya daga cikin furudusoshi mata da ake ji da su a da.fim din Sahnafahna, daya daga cikin finafinanta da suka yi tashe a karkashin kamfaninta na Kumbo Productions.

Sani Mu’azu: Koda yake ya yi fice a shirye-shiryen talabijin inda yake fitowa a matsayin jarumi, Kamfaninsa na Lenscope Media da ke Jos ya kwanta dama a harkokin Kannywood. A baya sun yi finafinai da kuma samar da mawaka a masana’antar.

Alhaji Ibrahim Mandawari: Shi ne shugaban Kamfanin Mandawari Enterprises da ya shirya finafinai da dama irin su Zakaran Gwajin Dafi da Marainiya da Gaskiya Dokin Karfe.

Aminu Mirror: Aminu Mirror fitaccen furodusa ne a Zaria, wanda ya yi fice musamman a tsakanin 2000s, sai dai an dain jin ɗuriyarsa tun rasuwar abokinsa Ahmed S. Nuhu. Daga cikin finafinan da ya shira a Kamfanin Ijaba Productions akwai Ibro Police da Sirri ne.

Sai ya sake dawowa a fim din Gidan Badamasi mai dogon zango a matsayin Malam Zaidu.

Aminu Bizi: Shi ne Shugaban Kamfanin Bizi Productions, kuma ya shirya finafinai irinsu tsohon dan siyasa da Baba Ari ya ja da sauransu.

Ahmed Bifa: Shugaban Kamfanin Bifa Productions. Ya shirya finafinai irinsu Kyandir da Bakar fuska.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: fina finan Kannywood Hamisu Iyantama Ibrahim Mandawari kannywood a shirya finafinai a masana antar da ya shirya a karkashin

এছাড়াও পড়ুন:

Trump zai haramta wa ’yan Najeriya da wasu ƙasashe zuwa Amurka

Shugaban Amurka Donald Trump, ya bayyana cewa yana shirin daina karɓar mutane daga “ƙasashe masu tasowa” gaba ɗaya, ciki har da Afirka, Asiya da sauransu.

Ya bayyana haka ne yayin wani taro da ya gudana a fadar shugaban Amurka.

Ƙasar Japan ta fara sayar da i njin da ke yi wa mutane wanka

A cewarsa, tsohon tsarin shige da fice na Amurka yana rage ƙarfin tsaron ƙasa kuma yana matsa wa makarantun gwamnati, asibitoci, da sauran hidimomin jama’a.

Trump ya ce yawan baƙin haure a Amurka ya kai mutane miliyan 53, sannan ya yi zargin cewa mutane daga ƙasashen da ke fama da rikice-rikice, laifuka, da miyagun ƙungiyoyi suna ta zuwa ƙasar.

Ya ce shigowar baƙi ya kawo rabuwar kawuna da matsaloli a Amurka.

Haka kuma ya yi zargin cewa masu katin zama ’yan ƙasar da ke da tsarin ƙaramin albashi na rikice-rikice.

Ya batar da misali da Jihar Minnesota, yana inda ’yan gudun hijira daga Somaliya suka cika ta

Ya ce “ci gaban ƙasa ya lalace,” amma ya bayyana matakan da zai ɗauka.

Ya kuma ce zai soke shiga ƙasar ba bisa ƙa’ida ba wanda gwamnatin Biden ta bari ke faruwa.

Trump, ya ce burinsa shi ne rage yawan waɗanda yake ganin ba su da tasiri mai kyau ko kuma suna kawo matsala a ƙasar.

Ya ce “mayar da mutane ƙasashensu” shi ne kawai mafita mai ɗorewa.

Wannan sanarwa na zuwa ne bayan harin da aka kai a Washington, D.C, inda aka yi wa sojoji biyu rauni.

Hukumomi a ƙasar sun ce mutumin da ake zargi da kai harin, ya shiga Amurka a 2021 bayan ya taimaka wa sojojin ƙasar a Afghanistan, kuma an ba shi mafaka.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Nijar : zamu sayar da uranium dinmu ga wanda muka ga dama_ Janar Tiani
  • Lebanon: Wasikar Kungiyar Hizbullah Ga Paparoma
  • ’Yan bindiga sun kashe tsohuwa, sun sace mutum 3 a Kano
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 163
  • Kamfanin Kera Jiragen Sama Na Airbus Ya Bukaci  A Dawo Da Jiragen Sama Samfrin  A320 Saboda Gyara
  • Yadda ’yan mata ke kuɗancewa da kasuwancin fara a Kano
  • Yadda ’yan mata ke kufancewa da kasuwancin fara a Kano
  • Portugal ta lashe Kofin Duniya na ’yan ƙasa da shekaru 17 a karon farko
  • Trump zai haramta wa ’yan Najeriya da wasu ƙasashe zuwa Amurka
  • Ƙasar Japan ta fara sayar da injin da ke yi wa mutane wanka