An Yi Gagarumin Taron Ashura A Birnin Beirut Na Kasar Lebanon
Published: 6th, July 2025 GMT
Dubun dubatar mutanen kasar Lebanon sun yi gangamin raya ranar Ashura ta shahadar Imam Hussain ( a.s) a unguwar Dhahiya wacce aka sauya wa suna suna unguwar Shahid Sayyid Hassan Nasrallah.
Mahalarta taron sun daga hotunan Sayyid Hasrallah wanda a shekarar da ta wuce yana raye, ya kuma gabatar da jawabi a wurin jimamin Ashura.
A yau 10 ga watan Muharram ne dai al’ummar musulmi Mabiya mazhabar Ahlul bayti suke tunawa da shahadar Imam Hussain ( a.s) da iyalansa da kuma sahabbansa madaukaka.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
Masanin Kenya: Kasashe Masu Tasowa Suna Bukatar Kasar Sin
Masanin Kenya kan huldar kasa da kasa mai suna Cavince Adhere, ya bayyana a yayin zantawarsa da dan jarida na kamfanin dillancin labarai na Xinhua a kwanan nan cewa, a matsayinta na daya daga cikin kasashe masu tasowa, hadin gwiwar Sin da kasashe masu tasowa ya jaddada daidaito da samun albarkatu, inda hakan ya samu aminci daga kasashe masu tasowa. Kuma har ila yau, hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kasashe masu tasowa ya riga ya samu gagarumin ci gaba, don haka makomar kasashe masu tasowa na bukatar ci gaba da kasancewar Sin a cikinsu.
Bugu da kari, Cavince Adhere ya jaddada cewa, Sin ta bayyana bukatun kasashe masu tasowa na duniya yadda ya kamata, kana tana inganta ra’ayoyin da suka dace da muradunsu, kamar yadda aka samu ci gaba da kuma bunkasa a tsarin BRICS. Cavince Adhere ya ce, “Ta hanyar kafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare, da zuba jari a fannin samar da ababen more rayuwa, da yin mu’amala da juna a fannin al’adu, da bullo da sabbin ra’ayoyi a fannonin raya kasa da kasa, Sin ta zama wani muhimmin karfi wajen gina tsarin dunkulewar kasa da kasa.”
Kazalika, ya ce, “Ko shakka babu, kasashe masu tasowa ma za su kasance wani karfi wajen inganta ci gaba mai dorewa a karni na 21.”(Safiyah Ma)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp