Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp.

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Shugaba Tinubu Ya Rantsar da Sabon Shugaban Hukumar Kidaya, Kwamishinoni da Manyan Sakatarori

Daga Bello Wakili

Shugaba Bola Tinubu ya rantsar da Shugaban Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC) da kwamishinoni biyu na hukumar, tare da sabbin manyan  sakatarori guda biyar da aka nada a gwamnatin tarayya.

Daga nan ya jagoranci taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Bayan karanta takardar tarihin rayuwarsu, manyan sakatarorin biyar Abdulkarim Ibrahim, Dr John Ezeamama, Dr Abdul-Sule Garba, Dr Isiaku Mohammed da Dr Ukaire Chigbowu, sun dauki rantsuwar kama aiki, sannan suka sanya hannu a kundin rantsuwa.

An kuma rantsar da Dr Aminu Yusuf, wanda shugaban kasa ya nada a matsayin Shugaban NPC a ranar 9 ga Oktoba, da kwamishinoni biyu ciki har da Dr Tonga Betara daga Jihar.

NPC ita ce hukuma da ke da alhakin gudanar da kidayar jama’a a hukumance, yin rajistar haihuwa da mace-mace, da tattara bayanan kimiyyar jama’a domin tsare-tsare.

Majalisar ta yi shiru na minti guda domin tunawa da tsohuwar Ministar Harkokin Waje, Ambasada Joy Ogwu, wadda ta rasu a ranar Litinin, 13 ga watan Oktoban 2025 tana da shekaru 79.

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Mutum 3 sun mutum yayin haƙar rijiya a Kano
  • Amurka ta Faɗaɗa Jerin ƙasashen Afrika Da ta Sanya wa Takunkumin Visa
  • Limamin Tehran:  Idan Abokan Gaba Su Ka  Sake Yin Kuskure Akan Iran Za Su Sake Cin Kasa
  • Fadlallah Na Hizbullah Ya Yi Kiran Hadin Kai A Tsakanin Musulmi Da Larabawa Domin Fuskantar Kalubale
  • Shugaba Tinubu Ya Rantsar da Sabon Shugaban Hukumar Kidaya, Kwamishinoni da Manyan Sakatarori