Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Kwamishinan Ganduje Kan Zargin Ɓatan N240m
Published: 18th, March 2025 GMT
Alƙalin kotun, Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu, ta bayar da umarnin kama Lawal tare da ɗage shari’ar zuwa ranar 6 ga watan Mayu.
A wata shari’a daban, kotun ta kuma bayar da umarnin kama Jibrilla Muhammad, tsohon Manajan Darakta na Kamfanin Zuba Jari da Kadarorin Kano (KSIP), bisa zargin ɓatan Naira miliyan 212.
A gefe guda ta sake ɗage zaman wannan shari’a saboda abokin shari’ar tasa, Dauda Sheshe, har yanzu bai karɓi sammaci ba.
An ɗage shari’arsu zuwa ranar 29 ga watan Afrilu.
Dukkanin waɗannan shari’u na da alaƙa da zargin karkatar da kuɗaɗen jama’a yayin da suke rike da muƙaman gwamnati.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Tsohon Kwamishina
এছাড়াও পড়ুন:
Makiyayi Ya Kashe Abokai 2 A Nasarawa Kan Rikicin Kiwo
Michael, wanda ke zaune a Phase 4, ya yi ƙoƙarin ceton abokinsa, amma shi ma makiyayin ya sare shi da adda.
An garzaya da Michael zuwa Asibitin Mararaba domin ceto rayuwarsa, amma likita ya tabbatar da mutuwarsa bayan isar su.
‘Yansanda sun bayyana cewa an adana gawar Michael a asibitin domin gudanar da bincike.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, ya umurci a tura jami’an tsaro domin kare rayuka da dukiya a yankin, tare da umartar Mataimakin Kwamishinan Sashen Binciken Laifuka da ya fara bincike da kuma kamo wanda ake zargi domin gurfanar da shi a kotu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp