Sanatan ya bayyana cewa gwamnonin yankin na farko sun ba da gagarumar gudunmuwa wajen jagorantar hadin kai wajen cimma muradun yankin daga kan ikon sarrafa albarkatun kasa zuwa matsalolin muhalli da sauransu.

A kan wannan ya yi kira ga gwamnoni.masu ci a yanzu da su ci gaba da wannan al’adar, kuma su kara kokari kan ciyar da yankin a gaba.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Gyaran Kundin Tsarin Mulki

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnan Bauchi ya ƙaddamar da kwamitin ƙirƙiro da sabbin masarautu

Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya ƙaddamar da wani babban kwamitin ƙirƙiro masarautu da gundumomin hakimai a jihar.

An ƙaddamar da kwamitin ne a wani mataki na magance buƙatu da dama daga al’ummomi daban-daban da kuma inganta al’adu da tsarin mulki na asali a faɗin Jihar Bauchi.

Abba ya naɗa Ahmed Musa a matsayin Babban Manajan Kano Pillars An gano wasu bama-bamai 56 da ISWAP suka binne a Borno

Gwamna Bala ya shaida wa kwamitin da ya sake duba buƙatu na samar da sabbin masarautu a faɗin jihar.

Ya ce, aikin kwamitin shi ne inganta harkokin gudanar da mulki na cikin gida da inganta al’adu da kuma ƙarfafa muhimmiyar rawar da sarakuna ke gudanarwa wajen haɗin kai da ci gaba.

Gwamnan ya bayyana matakin a matsayin alƙawarin da gwamnatinsa ta yi na tabbatar da adalci da haɗa kai da kuma ƙarfafa tsarin mulki da ci gaba a Jiha da ƙananan hukumomi.

Ya bayyanawa kwamitin da ya ba da shawarar al’ummomin da suka cancanta na sabbin masarautu, da ba da shawarar tsarin gudanarwa don ingantaccen aiki na sabbin masarautu, masarautu ko gundumomi da gabatar da cikakken rahoto tare da shawarwari masu dacewa cikin makonni takwas.

Gwamnan ya buƙaci kwamitin da ya gudanar da aikinsa cikin gaskiya da himma da kuma adalci.

Ya bayyana cewa, shirin na cika alƙawuran siyasa ne da nufin karkatar da hukumomi don samar da ingantattun ayyuka da kuma ƙara rarraba albarkatu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Sanata Dickson Ya Buƙaci ‘Yan Nijeriya Da Su Yi Yaƙi Da Matsalar Sayen Ƙuri’a
  • Ranar Talata Mai Zuwa Zan Koma Zauren Majalisar Dattawa – Sanata Natasha
  • Ku Manta Da 2027, Tinubu Zai Ci Gaba Da Mulki Har 2031 — Fadar Shugaban Ƙasa Ga ADC
  • Gidajen Gala Ne Kadai Mafita Ga Masana’antar Kannywood – Falalu Dorayi
  • Gwamnan Bauchi ya ƙaddamar da kwamitin ƙirƙiro da sabbin masarautu
  • Abba Ya Yi Sabbin Naɗe-naɗe A Jihar Kano
  • Sojoji sun kashe ’yan ta’adda da ƙwato makamai a Borno
  • ‘Yan Nijeriya Na Kewar Buhari Saboda Azabar Da Suke Fuskanta A Hannun Tinubu – Amaechi
  • ‘Yan Nijeriya Na Kewar Gwamnatin Buhari Saboda Azabar Da Suke Fuskanta A Hannun Tinubu – Amaechi