NAJERIYA A YAU: Yadda Mai Karamin Karfi Zai Mallaki Muhalli Da Kudi Kalilan
Published: 18th, March 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Mallakar Muhalli na ɗaya daga cikin burin kowanne ɗan Najeriya.
Sai dai wannan buri a mafi yawan lokacin baya cika musamman ga masu matsakaitan samu.
Ƙananan ma’aikata da mafi ƙarancin albashin su yake naira dubu saba’in ba zai ciyar da su, ko tufatar da su ba, ballantana har su yi tunanin mallakar muhalli nasu na ƙashin kansu.
Sai dai masana na bayyana cewa marasa karfin ma na iya mallakan nasu muhallin daidai ruwa daidai tsaki.
NAJERIYA A YAU: Guraben Ayyukan Da Aka Kasa Cikewa A Najeriya DAGA LARABA: Asalin Tashe Da Tarihinsa A Ƙasar Hausa?Shirin Najeriya A Yau na wannan rana zai yi nazari ne kan hanyoyin da mai ƙaramin ƙarfi zai bi don mallakar muhalli a Najeriya.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Nijeriya
এছাড়াও পড়ুন:
Tawagar Majalisar Amurka ta iso Nijeriya Don Bincika Zargin Tauye Haƙƙin Addini
Majalisar Dokokin Amurka ya iso Abuja yayin da ƙasashen biyu ke ƙara matsa ƙaimi wajen tattaunawar diflomasiyya kan haɗin gwiwar tsaro da kuma zargin tauye haƙƙin addini.
Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan tsaro Nuhu Ribadu, ya ce ya gana da wakilan kuma zuwan tawagar na cikin abubuwan da suka amince da shi a tasu ziyarar da suka kai birnin Washington a watan Nuwamba.
“Tawagar ta ƙunshi ‘yanmajalisar wakilai Mario Díaz-Balart, Norma Torres, Scott Franklin, Juan Ciscomani, da Riley M. Moore,” in ji Ribadu cikin wata sanarwa a shafinsa na sada zumunta.
Kazalika, Jakadan Amurka a Najeriya Richard Mills na cikin tawagar.
A cewar Ribadu, tattaunawar ta mayar da hankali kan yaƙi da ta’addanci, tabbatar da zaman lafiyar yanki da kuma ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro tsakanin Nijeriya da Amurka.