Aminiya:
2025-11-02@21:10:42 GMT

An kama miyagun kwayoyin N300m da mutane 650 a Kano

Published: 13th, April 2025 GMT

Jami’an tsaro sun kwace miyagun kwayoyi da kudinsu ya kai Naira miliyan 300 sannan ta kama mutane 650 da ake zargi a Jihar Kano.

Kwamitin Dawo da Zaman Lafiya da Kyautata Dabi’un Matasa ta Jihar Kano ce ta yi wanna kame a fadin jihar, kamar yadad ta bayyana a rahotonta.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Ibrahim Bakori, ya bayyana, ya bayana cewa mutum 150 daga ckin adadin an kama su ne kan laifukan dabanci da kwacen wayada da dangoginsu.

Kwamitin ya ce aikin haɗin gwiwar, ya yi wannan nasara ne bayan da suka kai samame a kan maboyar masu aikata laifuka da aka gano a kananan hukumomi takwas da ke garin Kano.

An sake kama wasu mafarauta ’yan Kano a Jihar Edo ’Yan bindiga sun kona masallacin Juma’a da asibiti da gidaje da Zamfara Badaƙalar Miyagun Ƙwayoyi: Kotun Amurka ta ba da umarnin fitar da bayanai kan binciken Tinubu

Hukumar ta bayyana cewa an gudanar da aikin ne tare da ’yan sanda da Hukumar Yaki da Miyagun Kwayoyi (NDLEA) da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (NSCDC) da Hukumar Kula da Gidajen Yari da Hukumar Shige da Fice, da sauran hukumomi.

Da yake jawabi a wani taro da masu ruwa da tsaki a harkar tsaro, Shugaban Rundunar, Dakta Yusuf Ibrahim, ya ce ƙwace miyagun ƙwayoyin da aka kiyasta kimarsu a Naira miliyan 300 zai taka muhimmiyar rawa.

Ya kuma jaddada muhimmiyar rawar da tallafin al’umma ke takawa wajen dorewar ƙoƙarin Rundunar na inganta tsaron jama’a.

Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Aminu Abdussalam, ya yaba wa nasarorin da Rundunar ta samu, yana mai tabbatar da kudurin gwamnatin jihar na magance ƙalubalen tsaro ta hanyar irin waɗannan matakai masu ƙarfi. Sa’annan ya jaddada buƙatar haɗin gwiwa tsakanin hukumomi da al’umma don samun ɗorewar tsaro.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kano,  ya yaba da ingancin ayyukan da aka gudanar bisa ga bayanan sirri, yana amai kira da a kafa wata kotu ta musamman domin hanzarta shari’ar waɗannan laifuka.

Kwamandan Hukumar NDLEA na Jihar, Abubakar Idris, ya yaba da haɗin gwiwar da ke tsakanin hukumomin tsaro kuma ya yi kira da a ci gaba da shidon magance matsalolin tsaro a Jihar Kano.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: kwayoyi

এছাড়াও পড়ুন:

Tsaro: Taimakonmu Amurka ya kamata ta yi maimakon barazana — Kwankwaso

Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana damuwarsa kan kalaman da Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi game da Najeriya.

Kwankwaso, ya yi wannan magana ne bayan Trump ya yi barazanar ɗaukar matakin yaƙi game da zargin kisan kiyashi da ake yi wa Kiristoci.

Kisan Kiristoci: Ba zan yaƙi ƙasar iyayena kan labaran ƙarya ba — Sojan Amurka Kisan Kiristoci: Lauyoyi sun nemi Gwamnatin Tarayya ta tattauna da Amurka

A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Kwankwaso, ya ce Najeriya ƙasa ce mai cikakken ’yanci, wadda ke fama da matsalar tsaro daga miyagu a sassa daban-daban na ƙasar.

“Matsalar tsaron da muke fuskanta ba ta bambanta tsakanin addini, ƙabila ko ra’ayin siyasa,” in ji shi.

Ya buƙaci gwamnatin Amurka da ta tallafa wa Najeriya da sabbin fasahohi domin yaƙar matsalar tsaro maimakon yin kalaman da za su iya raba kan ’yan ƙasa.

“Amurka ya kamata ta taimaka wa hukumomin Najeriya da ingantattun fasahohi don magance matsalolin tsaro, maimakon yin barazanar da za ta ƙara raba ƙasar,” in ji Kwankwaso.

Haka kuma, ya shawarci Gwamnatin Najeriya da ta naɗa jakadu na musamman domin inganta hulɗar diflomasiyya da Amurka da kare muradun ƙasar a matakin duniya.

Ya kuma yi kira ga ’yan Najeriya da su zauna lafiya, inda ya bayyana cewa wannan lokaci ne da ya dace a fifita haɗin kan ƙasa ba abin da ke raba ta ba.

“Wannan lokaci ne da ya kamata mu mayar da hankali kan abin da zai haɗa kanmu ba wanda zai raba mu ba. Allah Ya albarkaci Najeriya,” in ji shi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gidauniyar IRM Da KADCHMA, Ta Ƙaddamar Da Inshorar Lafiya Kyauta Ga Mutane 200 A Kaduna
  • Tsaro: Taimakonmu Amurka ya kamata ta yi maimakon barazana — Kwankwaso
  • Dalilin Da Ya Sa Hukumar NIWA Ta Fara Gyaran Hanyoyin Ruwa A Jihar Legsa
  • Gwamna Namadi Ya Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda
  • Gwamnatin Jigawa Ta Bada Motocin Aiki Goma Ga Rundunar ‘Yan Sanda
  • Gwamna Uba Sani Ya Gabatar Da Kudirorin Raya Jihar Kaduna A Taron Ƙoli Na Biranen Asiya A Dubai 
  • Ranar Foliyo Ta Duniya: Muna Fatan Ganin Karshen Cutar Foliyo A Jihar Katsina -Zulaihat Dikko Radda
  • Matsalar Talauci Da Rashin Tsawon Rai Da ‘Yan Nijeriya Ke Fuskanta
  • An sake kama shi a cikin ’yan fashi kwana 5 da fitowa daga kurkuku
  • Matsalar Tsaro: Ko Sabbin Shugabannin Rundunar Soji Za Su Kawo Sauyi?