A yau daya ga watan Maris ne dokar haramta amfani da tankunan dakon man fetur masu daukar lita 60,000 saboda yawan hatsarin da suke yi, wanda kuma yake lakume rayukan daruruwan mutane a ko wace shekara a duk fadin kasar.

Jaridar Weeken Trust ya bayyana cewa hukumar ‘ The Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory Authority (NMDPRA)’ ta haramta amfani da iran wadannan tankunan man ne daga yau Asabar 1 ga watan Maris, saboda ceton rayukan mutanen kasar.

Dokar dai zata shafi ayyukan mutanen, don wasu zasu rasa ayyukansu.

Dokar ta kara da cewa, daga yau tankunan man masu daukar lita 45,000 zuwa kasa ne kawai za’a a barisu dauki man fetur zuwa wasu wurar daga deport.

Sai kuma kungiyar masu dakon man fetur a kasar sun bayyana cewa zasu yi asarar tankuna na kimani   naira biliyon 300 saboda wannan haramcin.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Hukumar Kula da Da’ar Ma’aikata Za Ta Fara Daukar Bayanai Ta Yanar Gizo

Hukumar kula da da’ar ma’aikata ta sanar da cewa, a halin yanzu ana iya  bayyana kadarorin ma’aikatan ta hanyar yanar gizo, wani mataki da aka tsara domin saukaka aikin da kuma kara yin lissafi.

 

Daraktan ofishin na jihar Jigawa Abubakar Bello ne ya bayyana haka a lokacin da ya ziyarci shugaban ma’aikatan jihar Alhaji Muhammad K. Dagaceri a ofishin sa.

 

Abubakar Bello ya jaddada cewa sabon shirin na da nufin rage dinbin aikin dake gaban ma’aiakata da kuma saukaka tantance kadarorin domin yaki da cin hanci da rashawa a cikin tsarin.

 

“Mun sauya dabara zuwa rajista ta yanar gizo don bayyana kadarorin, muna ba wa mutane damar kammala aikin daga gidajensu. Duk da haka, muna neman goyon bayan ku don tabbatar da cewa an sanar da jami’an gwamnati tare da karfafa gwiwar su bi wannan sabon tsari,” in ji shi.

 

Da yake mayar da jawabi, shugaban ma’aikata na jiha Alhaji Muhammad K. Dagaceri, ya yi alkawarin wayar da kan jami’an gwamnati cikin tsanaki game da muhimmancin bayyana kadarorin su, kamar yadda hukumar da’ar ma’aikata ta ba su umarni.

 

Ya tunatar da cewa rashin yin biyayya ga kundin tsarin mulkin kasa ne.

 

Dagaceri ya bada tabbacin bada goyon baya da hadin kai domin cimma burin da ake so na wannan shiri.

 

USMAN MZ

 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • INEC Ta Gudanar da Taron Masu Ruwa da Tsaki Kafin Zaɓen Cike Gurbi na Babura/Garki
  • NNPCL ya sake haƙa sabbin rijiyoyin man fetur 4 a Kolmani
  • Kamfanin NNPCL ya sake haka sabbin rijiyoyin man fetur 4 a Kolmani
  • Majalisar Kasa Na Duba yiwuwar Dawo Da Gwamnan Jihar Rivers Fabura Kafin Cikar Wa’adin Watanni Shida.
  • Hukumar Kula da Da’ar Ma’aikata Za Ta Fara Daukar Bayanai Ta Yanar Gizo
  • Wasu ’yan siyasa na sukar Tinubu saboda ɗan Kudu ne — Onanuga
  • Siriya Da HKI Zasu Gudanar Da Taro A Baku
  • Manyan makarantu 2 ne kacal ke da rajista a Katsina — Gwamnati
  • Fiye Da Kamfanoni 30,000 Masu Zuba Jari Daga Waje Aka Kafa A Sin A Rabin Farkon Bana
  • EU Tace Zata Dakatar Da HKI Daga Cibiyar Bincikenta Saboda Gaza