Leadership News Hausa:
2025-11-02@17:19:57 GMT

Ba Zai Manta Da Shawarar Mahaifinsa Ba

Published: 15th, June 2025 GMT

Ba Zai Manta Da Shawarar Mahaifinsa Ba

Mahaifin Xi Jinping, Xi Zhongxun, ya taba shaida masa cewa, “Duk irin kololon matsayin da ka kai, kada ka manta da yi wa jama’a aiki tukuru, ka yi tunani game da jama’a, ka yi cudanya da jama’a, kuma ka zama wanda za a iya kusantarsu.”

A sakamakon haka, Xi Jinping ya mayar da shawarar mahaifinsa a matsayin alkiblar neman tabbatar da “cikar burin jama’a na samun ingantacciyar rayuwa.

” (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Sin Da Amurka Suna Taimaka Wa Juna Da Samun Wadata Tare

A ranar 30 ga wata ne shugabannin kasashen Sin da Amurka suka gana da juna a birnin Busan na kasar Koriya ta Kudu, lamarin da ya jawo hankulan kasa da kasa, inda shugabannin 2 suka yi musayar ra’ayoyi dangane da huldar da ke tsakanin kasashen 2 da al’amuran da suka jawo hankulansu. Sun amince da inganta hadin gwiwar kasashen 2 a fannonin tattalin arziki da cinikayya da makamashi da kyautata mu’amalar al’adu.

A yayin ganawar, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya jaddada cewa, yana son hada kai da shugaba Donald Trump na Amurka wajen aza harsashi mai kyau na raya huldar da ke tsakanin kasashen 2, tare da samar wa juna kyakkyawan yanayin samun ci gaba. A nasa bangaren, shugaba Trump ya ce, kasar Sin, abokiyar Amurka ce mafi girma. Kasashen 2 za su hada kansu wajen samun nasarar gudanar da manyan ayyuka da dama a duniya. Nan gaba Amurka da Sin za su kara samun nasara a hadin gwiwarsu. Shugabannin 2 sun amince su rika yin mu’amala da juna. Shugaba Trump yana sa ran kai ziyara a kasar Sin a farkon shekara mai zuwa, ya kuma gayyaci shugaba Xi ya ziyarci Amurka.

Masharhanta sun yi nuni da cewa, ganawar shugabannin 2 ta sanya tagomashi kan kyautatuwar huldar da ke tsakanin Sin da Amurka, ta kuma tsara manufar raya huldar kasashen 2 a nan gaba, tare da kwantar da hankulan kasashen duniya.

Abubuwan tarihi da kuma hakikanin abubuwa sun nuna cewa, wajibi ne Sin da Amurka su zama abokan juna. A wannan muhimmin lokaci, ganawar da shugabannin kasashen 2 suka yi ta sake tsara manufar kyautata da raya huldar da ke tsakanin kasashen 2. Muddin kasashen 2 suka aiwatar da muhimman daidaito da shugabannin 2 suka cimma, da mutunta ruhin adalci, tare da martaba juna da samun moriyar juna, to, za a raya huldar da ke tsakanin kasashen 2 ba tare da wata matsala ba, da kuma kara samar da kwanciyar hankali da tabbaci a duniya. (Tasallah Yuan)

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Xi Jinping Ya Halarci Kwarya-Kwaryan Taron Shugabannin APEC Na 32 Tare Da Gabatar Da Jawabi October 31, 2025 Daga Birnin Sin An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Tattaunawa Kan Kirkire-kirkire Da Bude Kofa Da Raba Damar Samun Ci Gaba A Colombo October 30, 2025 Daga Birnin Sin Sin Ta Fitar Da Jerin Sakamakon Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Tawagar Kasar Da Ta Amurka Suka Cimma  October 30, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Jamus ta shiga sahun ƙasashen da ke neman kawo ƙarshen yaƙin Sudan
  • Xi Jinping Ya Tattauna Da Shugaban Koriya Ta Kudu Lee Jae-myung 
  • Kofin kofi mafi tsada a duniya ya shiga kasuwa a kan Naira miliyan 1.5m
  • Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace
  • Barcelona ta shiga zarwacin Victor Osimhen
  • Sin Da Amurka Suna Taimaka Wa Juna Da Samun Wadata Tare
  • Xi Jinping Ya Halarci Kwarya-Kwaryan Taron Shugabannin APEC Na 32 Tare Da Gabatar Da Jawabi
  • Ana zargin ɗa da kashe mahaifinsa a Kano saboda hana shi ƙara aure
  • An Gudanar Da Taron Kasa Da Kasa Na Tattaunawa Kan Kirkire-kirkire Da Bude Kofa Da Raba Damar Samun Ci Gaba A Colombo
  • Gwamnatin Gombe ta saurari ra’ayoyin jama’a kan kasafin kuɗin 2026