HausaTv:
2025-07-31@14:23:32 GMT

Iran Ta Cilla Makamai Kan HKI Da Rana A Karon Farko A Yau Lahadi

Published: 15th, June 2025 GMT

Sojojin kasar Iran sun cilla makamai masu linzami da kuma jiragen yaki wadanda ake sarrafasu daga nesa kan HKI a dazuda nan nan, wayo yau lahadi a ci gaba da musayar wauta da suke yi da sojojin HKI kwanaki uku da suka gabata.

Kamfanin dillancin  labaran kare kai na kasar Iran Tasnim ya nakalto sojojin kasar na cewa sun cilla makamai masu linzami da Drones a karon farko da rana ido na ganin ido a kan HKI kuma tuna makaman sun fada a inda yakamata su fada a cikin haramtacciyar kasar.

A safiyar ranar jumma’a ce sojojin HKI suka kai hare-hare kan birnin Tehran inda suka kai manya-manyan jami’an sojojin kasar ga shahada, sannan suka kashe mutane fararen hula wadanda basu da laifi.

Bayan haka ne sojojin JMI suka fara maida martani a daren Asabar da daren lahadi, amma a wannan karon sun kai hare haren ne da ranar Lahadi ido na ganin ido.

Hare-haren wadanda aka basu suna “Alkawalin gaskiya Na 3 zasu ci gaba matakar HKI ta ci gaba da kaiwa Iran hare hare.

উৎস: HausaTv

এছাড়াও পড়ুন:

Sojojin Sin Sun Bi Sahun Shiga Ayyukan Ba Da Agajin Ambaliyar Ruwa

Rundunar sojojin ‘yantar da jama’ar kasar Sin, da rundunar ‘yan sandan kasar masu dauke da makamai, da dakarun sa-kai na cikin gida sun aike da dakaru domin shiga ayyukan ba da agajin gaggawa a yankunan da ambaliyar ruwa ta shafa a kasar Sin.

A baya-bayan nan ne aka tafka ruwan sama kamar da bakin kwarya a gabashi, da arewaci, da arewa maso gabas na kasar Sin, lamarin da ya haddasa ambaliya da sauran ibtila’i na zaftarewar kasa da suka yi sanadin asarar rayuka da dukiyoyi.

Rundunar ‘yan sanda masu dauke da makamai ta birnin Beijing ta aike da jami’ai da sojoji sama da 2,000 don taimaka wa ayyukan ba da agajin, inda aka kwashe sama da mazauna yankin da abin ya shafa 4,100 tare da kai akwatunan kayayyakin agaji fiye da 3,000 da tsakar ranar yau Talata. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  •  Sojojin Sahayoniya Suna Ci Gaba Da Kisan Kiyashi A Gaza
  • Hare-hare: ’Yan bindiga sun raba mutum 5,000 da muhallansu a Katsina
  • Sojojin Yemen Sun Kai Zafafan Hare-Hare Kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila Guda Uku  
  • Rashin Nasarar DPP A Zagayen Farko Na Kuri’ar Kiranye Ya Nuna Rashin Amincewar Al’ummar Taiwan Da Salon Mulkin Jami’yyar
  • Sojojin Sin Sun Bi Sahun Shiga Ayyukan Ba Da Agajin Ambaliyar Ruwa
  • Sojojin HKI Sun Ci Gaba Da Kashe Kawunansu
  • Kasar Iran Ta Musanta Yin Katsalandan A Tattaunawar Neman Tsagaita Bude Wuta A Gaza
  • Kasar Faransa Ta Yi Allah Wadai Da Harin Ta’addancin Da Aka Kai Birnin Zahedan Na Kasar Iran
  • Jami’an Tsaron Katsina Sama Da 100 Sun Rasu A Yaƙi Da ‘Yan Ta’adda – Gwamnati
  • Iran Ta Ce Amurka Ce Bayan Hare-haren Da Aka Kai Zahidan