An tallafa wa mata 250 da abinci da kayan sana’a a Kaduna
Published: 15th, June 2025 GMT
Wata ’yar kasuwa mai taimakon al’umma, Barista Catherine Bitrus, ta raba wa mata 250 da abinci da kayan sana’a a garin Manchok da ke Ƙaramar Hukumar Kaura, a Jihar Kaduna.
Tallafin ya haɗa da injinan niƙa, buhunan shinkafa, katan-katan na taliyar yara, da man girki.
Harin Benuwe: ’Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga Takarar Tinubu: Rikici ya ɓarke a APC bayan Ganduje ya ƙi goyon bayan ShettimaA lokacin rabon kayan, Catherine, shugabar kamfanin Natural Beauty Secret, ta ce ta yi hakan ne domin taimaka wa matan karkara da ke fama da matsaloli a rayuwa.
“Allah Ya ba ni arziƙi, shi ya sa na ga dacewa na raba da waɗanda ke bukata,” in ji ta.
“Na zaɓi mata ne domin na san irin wahalar da suke sha.”
Ta roƙi matan da su dage da ƙoƙari, ka da su yanke ƙauna, domin komai na duniya yana da mafita idan aka jajirce.
Catherine ta ce tana da niyyar ci gaba da wannan aiki, kuma ta yaba wa Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, saboda irin goyon bayan da yake bai wa mata a jihar.
Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na jihar, Barista James Kanyip, ya yaba da wannan aiki, inda ya buƙaci sauran masu hali da ƙungiyoyin su dinga tallafa wa marasa ƙarfi.
Shugaban kwamitin shirya taron, Lucky Ezra, ya bayyana Catherine a matsayin mace mai zuciyar taimako da kishin jama’a.
A madadin sauran matan da suka amfana, Josephine Bature ta nuna farin ciki da godiya, tare da addu’ar Allah Ya saka wa Catherine da alheri.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yar Kasuwa Kayan abinci Kayan Sana a
এছাড়াও পড়ুন:
Tinubu Ya Taya Amusan Da Gumel Murnar Samun Nasarori A Ɓangarori Daban-daban
Shugaban ya yaba da abinda ya kira kwarewa da juriya irin na Amusan, tare da cewa aikinta ya sake misalta irin daukakar da yan Nijeriya za su iya samu ta hanyar aiki tukuru da nuna kwazo, Tinubu ya yi fatan Gumel da Amusan su ci gaba da samun nasara a ayyukansu tare da ba su tabbacin gwamnati za ta ba su cikakken goyon baya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp