NATE Ta Rantsarda Sabbin Shugabanni Reshen Jihar Kaduna
Published: 13th, April 2025 GMT
Kungiyar Kwararrun Masu Fasahar Injiniya ta Ƙasa (NATE) ta rantsar da sabbin shugabannin reshen Jihar Kaduna da za su jagoranci harkokin kungiyar a jihar.
Mataimakin Shugaban Yankin Arewa maso Yamma na NATE, Injiniya Bala Muhammad, yayin bikin rantsarwa da aka gudanar a Kaduna, ya bukaci sabbin shugabannin da su fifita haɗin kai da ci gaban ƙungiyar.
Sabbin shugabannin da aka rantsar sun hada da: Injiniya Audu John a matsayin Shugaba, AbdulKadir Julde a matsayin Mataimakin Shugaba, sannan Williams Okonkwu a matsayin Sakataren reshen.
Sauran su ne Sim Marca Maikege a matsayin Ma’ajin Kuɗi, AbdulGaniu Isah a matsayin Sakataren Kuɗi, da Racheal Ovbiagele a matsayin Sakataren Fasaha.
Haka kuma, Engr. Ishaya Buba daga Radio Nigeria Kaduna ya zama Jami’in Hulɗa da Jama’a, Khadijah Abdullahi a matsayin Ko’odinetan Mata, sannan Aliyu Ibrahim Usman a matsayin Sakataren Membobinsu.
Matsayin Mai Bincike (Auditor) da Mataimakin Sakatari suna nan a buɗe, ba a cike su ba tukuna.
A jawabinsa na kama aiki, sabon Shugaban, Injiniya Audu John, ya jaddada muhimmancin jajircewar mambobi, musamman ta fuskar biyan kuɗin zama dan kungiya da kuma kuden cigaba da zama dan kungiya wato (check-off dues).
Ya ce babu wata ƙungiya da za ta samu ci gaba idan ba tare da sadaukarwar mambobinta ba, kuma za su baiwa wannan bangare muhimmanci sosai.
Injiniya Audu John ya kuma bayyana shirin hadin gwiwa da manyan abokan hulɗa, musamman a sashen masana’antu, gwamnati da masu zaman kansu, domin tabbatar da cewa mambobin kungiyar sun samu wakilci da tallafi yadda ya kamata.
A cewarsa, shugabannin da suka gabata sun fara irin wannan aiki ta hanyar kai ziyarar girmamawa zuwa kamfanonin Nocaco Nigeria Limited da Hukumar Albarkatun Ruwa domin tantance mambobi da kuma farfado da hulɗar hadin gwiwa.
Shugaba Audu ya yaba wa Kwamitin Zaɓe karkashin jagorancin Engr. Silas Oluyori bisa gudanar da zaɓe mai tsafta, adalci da gaskiya duk da kalubalen da suka fuskanta.
A nasa jawabin, Mataimakin Shugaban Yanki Arewa maso Yamma, Injiniya Bala Muhammad, wanda Jami’in ƙasa na NATE, Injiniya Lukman Sani ya wakilta, ya bayyana cewa reshen Kaduna ne tushen dukkanin rassan NATE a yankin Arewa maso Yamma, amma har yanzu yana fama da kalubale.
Ya bukaci sabbin shugabannin su yi aiki tare da juna don dawo da karfin da kuzarin reshen Kaduna kamar yadda aka san shi a da.
Ya taya kwamitin zaɓe murna bisa gudanar da zaɓen cikin nasara, tare da tabbatar da ci gaba da tallafa musu don cigaban reshen jihar.
Tun da farko a jawabin sa, Shugaban Kwamitin Zaɓe, Engr. Silas Oluyori, ya gode wa duk masu ruwa da tsaki a kungiyar bisa goyon bayan da suka bayar, wanda ya taimaka sosai wajen shawo kan matsalolin da suka fuskanta a lokacin shirya zaɓen.
A zantawa da manema labarai, sabon Jami’in Hulɗa da Jama’a, Engr. Ishaya Buba, na gidan Radio Nigeria Kaduna ya bayyana cewa sabbin shugabannin za su kawo sauyi mai amfani wanda zai ɗaga darajar ƙungiyar zuwa mataki mafi girma.
Ya ce, cancanta da jajircewar sabbin shugabannin na nuna alamar cewa za su taka rawa ta kwarai wajen jagoranci da kawo ci gaba mai ma’ana ga reshen Kaduna.
REL: Adamu Yusuf
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: Gwamnati Kaduna Jihar Rantsarda
এছাড়াও পড়ুন:
Mataimakin Gwamnan Zamfara Ya Jajantawa Al’ummar Gumi
Mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Mani Malam Mumini ya jajanta wa al’ummar karamar hukumar Gumi kan mumunan al’amuran da suka salwantar da rayukan mazauna kauyen Fas su 19 a makonnin da suka gabata.
Malam Mumini ya bayyana haka ne a lokacin da ya jagoranci wasu jami’an gwamnati da suka kai ziyarar jaje ga al’umma, inda ya jajantawa iyalan wadanda abin ya shafa, da Majalisar Masarautar, da daukacin al’ummar Gumi.
Ya bayyana bala’in a matsayin mai raɗaɗi, yana mai jaddada cewa, gwamnatin jihar ta himmatu wajen magance matsalolin.
Mataimakin Gwamnan ya tuna cewa lamarin na farko ya faru ne a lokacin da mazauna kauyen cikin firgici kan harin da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne suka kai, suka shiga cikin wani jirgin ruwa wanda a karshe ya kife sakamakon kifewar da ya yi, wanda ya yi sanadin asarar rayuka da dama.
Ya kuma bayyana cewa, a yayin da bala’i na biyu ya faru kwanaki bayan wata motar bus ta Homa dauke da ‘yan daurin aure ta kutsa cikin kogin Gwalli a kan hanyar da ta wuce kan gada mai dauke da yashi, inda mutane 19 suka mutu.
Ya yi nuni da cewa, duk da cewa dan majalisar da ke wakiltar yankin ya gabatar da kudiri a kan munin yanayin gadar, amma har yanzu ana duba lamarin a lokacin da bala’in ya afku.
Mani Malam Mumini ya ce tuni gwamnatin jihar ta aike da tawagar injiniyoyi domin tantance gadar da kuma hanyoyin da suka hada da juna.
Wani shugaban al’umma a Gwalli ya yi kira da a kawo dauki cikin gaggawa tare da jaddada muhimman dabarun hana gadar ta ruguje nan gaba.
Shima da yake nasa jawabin mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara, Adamu Aliyu Gumi, ya bayyana wannan lamari a matsayin babban rashi ga al’umma, ya kuma yi kira da a gaggauta daukar mataki na gaggawa domin kaucewa afkuwar bala’o’i.
A yayin ziyarar, Mataimakin Gwamnan ya kuma kai gaisuwar ban girma ga Mai Martaba Sarkin Gumi, Mai Shari’a Lawal Hassan mai murabus, tare da jajanta masa bisa wannan al’amarin da aka samu.
A nasa jawabi, mai martaba Sarkin Gumi, Mai Shari’a Lawal Hassan ya bukaci gwamnatin jihar da ta hada kai da hukumar kula da hanyoyin ruwa ta kasa NIWA domin samar wa majalisar jiragen ruwa na zamani domin rage yawaitar hadurran jiragen ruwa.
Mai shari’a Hassan ya koka da cewa, kwalekwalen katako na gargajiya da ake amfani da su a halin yanzu ba su da tsaro kuma suna tabarbarewa cikin sauri, suna jefa rayuka cikin hadari.
Sarkin ya kuma yabawa gwamnatin jihar bisa kudurin da ta dauka na magance matsalar rashin tsaro da kuma kalubalen da ke addabar jihar.
Tun da farko, shugaban karamar hukumar Gumi, Aminu Nuhu Falale, ya kuma bukaci a kara kaimi wajen samar da tsaro musamman a yankin Birnin Magaji, saboda karuwar hare-haren ‘yan bindiga.
Ya bayyana cewa, hatsarin kwale-kwale na karshe ya samo asali ne sakamakon firgici yayin da mutanen kauyen suka yi yunkurin tserewa daga hannun ‘yan bindiga, lamarin da ya kai ga kifewar kwale-kwalen.
COV/AMINU DALHATU