Sojojin Kasar Iran Sun Ce Bazasu Dakatar Da Yaki ba Har Zuwa Samun Nasara A kan HKI
Published: 15th, June 2025 GMT
Babban kwamandan dokarun khatamul Ambiya (s) a nan birnin Tehran ya bayyana cewa sojojinsa zasu ci gaba da fafatawa da HKI har zuwa lokacinda zata dakatar da kawowa Iran yaki, ko kuma ta sami nasara a kansu,
Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto Janar Ali Shudmoni, yana fadar haka a yau Lahadi bayan da suke cilla makamai masu linzami da kuma jiragen yaki wadanda ake sarrafasu da nesa kan HKI a karon farko na rana, a cikin kwanaki uku da fara yakin.
Janar Shodmani ya kara da cewa zasu ci gaba da kaiwa yahudawan hare-hare har zuwa lokacinda zasu yi nadama sun daina yakin.
Kwamnatin ya bayyana cewa ya zuwa yanzu sun saminar kasar lalata cibiyoyin da jiragen yakin HKI suke shan makamashi wanda yake basu damar isa kasar Iran don kai hare-hare. Banda haka akwai nasarori da dama da suka samu a hare-haren wadanda nan gaba zasu bayyana.
উৎস: HausaTv
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan bindiga sun sace fasinjoji a cikin motocin bas a Kogi
Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da fasinjoji a cikin wasu motocin bas Toyota guda biyu a titin Itobe zuwa Ajegwu-Anyigba a Ƙaramar hukumar Ofu ta jihar Kogi.
An samu rahoton cewa, lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da misalin ƙarfe 5 na asubahi a tsakanin ƙauyukan Ojiwo’-Ajengo da Mamereboh da ke kan babbar hanyar.
Gwamnatin Yobe ta ƙaddamar da shirin amfani da ma’adanai Kotu ta dakatar da babban taron PDP na ƙasaAn ce masu garkuwa da mutanen sun yi amfani da wata tirela da aka kama wajen tare hanyar bayan shingen binciken jami’an tsaro, da ke kusa da wurin da lamarin ya faru.
Shedun gani da ido sun ce ɗaya daga cikin motocin bas ɗin mai lamba KG: KPA 622LG na kan hanyarta zuwa Abuja, tare da fasinjoji daga wata tashar mota a unguwar Ankpa da ke yankin Kogi ta Gabas.
Har yanzu ba a iya gano adadin fasinjojin da aka yi garkuwa da su ba zuwa yanzu, sai dai mun iya tabbatar da cewa ɗaya daga cikin motocin na ɗauke da fasinjoji ne daga yankin Ankpa, kamar yadda aka gano wasu takardu da wasu kayayyaki a wurin da lamarin ya faru suka bayyana.
“Motocin bas ɗin guda biyu suna kan hanyar Abuja ne a lokacin da suka ci karo da shingayen ’yan bindiga a safiyar ranar Alhamis. Dukkanin fasinjojin, ciki har da direban motocin bas ɗin biyu an yi awon gaba da su cikin daji,” in ji Unubi Ademu, wani mazaunin Achigili, a ƙauyen da ke maƙwabta.
Al’ummar yankin sun ƙara da cewa, jami’an tsaro da suka haɗa da sojoji da mafarauta da kuma ’yan banga suna ƙoƙarin magance lamarin.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan Jihar Kogi (PPRO), CSP William Aya bai amsa kira da saƙo ba lokacin da aka tuntuɓe shi har zuwa lokacin tattatara wannan rahoto.